Shekaru 3 bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, kasar Sin tana mayar da jama’arta da rayukansu a gaban kome. Ta kuma kyautata matakan yaki da cutar bisa lokaci da yanayin da ake ciki. Tana kuma raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa da kuma dakile yaduwar cutar a lokaci guda, tare da kiyaye rayuka da lafiyar jama’arta yadda ya kamata.
Daga karshen shekarar 2019 zuwa watanni 6 na farkon shekarar 2020, kasar Sin ta gano barkewar annobar a kan lokaci, inda ta tsai da kuduri mai muhimmanci na daukar matakin kulle a birnin Wuhan nan take ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya hana yaduwar cutar zuwa sauran sassan kasar, ta yadda Sin ta tabbatar da daidaiton dakile da kandagarkin cutar a duk fadin kasar, da yin iyakacin kokarin rage asarar rayukan jama’arta. Daga watanni 6 na farkon shekarar 2020 zuwa karshen shekarar 2022, kasar Sin ta yi wa al’ummarta mafi yawa a duniya allurar rigakafin cutar kyauta cikin gajeren lokaci, lamarin da ya sa yawan masu kamuwa da cutar da kuma yawan mutuwar mutane sakamakon cutar dukkansu suka fi kankanta a duniya.
A yayin da kasar Sin take daidaita matsaloli da dama, har kullum tana mara wa kasashen duniya baya wajen yaki da cutar ta COVID-19. Ta samar wa kasashe 153 da kungiyoyin kasa da kasa 15 daruruwan biliyoyin kayayyakin kandagarkin cutar. Ta kuma samar wa kasashe da yankuna fiye da 180 da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 10 fasahohin dakile da kandagarkin cutar da ba da jinya da kiwon lafiya. Kana kuma, kasar Sin ta tura kungiyoyin masana ilmin lafiya 37 zuwa kasashe 34, a kokarin samar da kyawawan fasahohinta na yaki da cutar ba tare da rufa-rufa ba. Har ila yau, kasar Sin ta samar wa kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120 alluran rigakafin cutar fiye da biliyan 2.2, hakan ya sa kasar Sin zama kasar da ta fi samar wa kasashen duniya alluran.
Tun daga watan Nuwamban shekarar 2022 da ta gabata, kasar Sin ta rika kyautata matakan yaki da cutar, bisa manufar “kiyaye lafiya da magance samun yawan wadanda ke fama da cutar mai tsanani”, ta kuma samu nasara cikin kankanin lokaci, inda aka yi wa mutane fiye da miliyan 200 jinya, tare da ceton wadanda ke fama da cutar mai tsanani kimanin dubu 800. Lamarin da ya sa yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya fi kankanta a duk duniya. Kasar Sin ta samu gagarumar nasarar yaki da cutar ta COVID-19, tare da yin abin al’ajabi a tarihin dan Adam. (Tasallah Yuan)