Assalamu alaikum jama’a barkanmu da sake haduwa a wannan satin inda za mu yi magana akan sayar da abubuwan sufuri.
Sufuri na da matukar muhimmanci wajen hada alaka tsakanin alummanmu a duk fadin duniya.
- Yadda Zaben Shugabannin Kungiyar Masu Maganin Gargajiya Ta Kasa Ya Gudana
- Dabarar Siyasa Ta Balan-balan Ta Amurka
Kuma ta kasu kashi biyu: Akwai sufuri a matsayin zirga-zirga, akwai kuma sufuri a matsayin sana’ar daukar jama’a ko kaya daga wuri zuwa wuri.
Yau za mu yi magana akan sufuri a matsayin daukar kaya daga guri zuwa guri.misali mutum zai iya sayen abubuwan sufuri kamar su mota, Adaidaita Sahu, babur mai kafa biyu kai har ma da keke da sayar da su hanya ce babba itama da take zuba jarin da mutum yake da shi ya zuba a kasuwancin saboda kusan kullum kara tashi suke yi kuma kara neman su ake.
Saboda idan mutum ya sayi mota ya kawo ta ‘yar Kwatano daga wata kasa zuwa wata kasa shifa irin wannan kasuwancin a basu ci riba ba shi ne su tashi da Naira 50,000 wanda fiye da haka ma ana samu a fannin.kuma fannin wannan sana’ar duka ya shafi ‘Second hand’ ne ko sabo wani Lokacin sayen sabon ya fi riba a saida wani kuma lokacin second din ne yake saye sai ya saida ya samu riba mai yawa bayan ya yi masa gyara idan da yana da matsala.
Hanyoyin sufuri na da yawa amma na motoci ya fi kyau da sufurin kasa ko kuma sufurin ruwa.
Allah ya ba da sa’a.