Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ne kaɗai ta bai wa iznin riƙa amfani da na’urar BVAS domin tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe gangariya.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara cibiyar horas da Jami’an Zaɓe da Mataimakan Jami’an Zaɓe na I da na II, ranar Asabar, a Abuja.
Yakubu ya ce INEC ba ta da isassun ma’aikatan da za su iya gudanar da zaɓe a faɗin ƙasar nan kuma a lokaci guda. Ya ce dalili kenan ta ke ɗaukar masu yi wa ƙasa hidima domin samar da sahihi kuma kuma karɓaɓben zaɓe ba tare da tashin hankula ba.
Shugaban ya gargaɗi matasan NYSC su nuna kishin Nijeriya da ‘yan Nijeriya, ba kishin wata jam’iyya ba.
Farfesa Yakubu ya kuma gargaɗi matasan cewa kada su yi kuskuren bai wa wani ajiya, tsaro ko kulawar na’urar tantance masu rajistar zaɓe, wato BVAS a hannun wani can daban.
Haka kuma ya ce kowane ɗan bautar ƙasa mai amfani da BVAS za a riƙa bibiyar sa ta lambar bibiyar ƙwaƙwaf, wato ‘code’ ko ‘tracker’.
Ya ce, “Nijeriya ta yi sa’a da gamo-da-katarin samun matasa irin ku. Saboda babu yadda INEC za ta iya shirya zabe ba tare da gagarimar gudummawar ku ba.
“Saboda haka mun dogara a kan ku da sauran ma’aikata. Amma ku ne za ku fi saura gudanar da aikin zaɓe mafi muhimmanci a rumfunan zaɓe. Saboda a can ne jama’a za su je su yi zaɓe. Kuma kowanen ku zai yi rantsuwar cewa ba zai goyi bayan kowace jam’iyyya ba.
“Kishin ku ya tsaya kan Nijeriya da ‘yan Nijeriya kaɗai, ba kan jam’iyya ba. Ku kasance ku ne tamkar shugabannin INEC a rumfunan zaɓen ku. Ku ne ma sarakunan daulolin rumfunan zaɓe.
“Ku kaɗai ne aka bai wa iznin sarrafa na’urar BVAS a ranar zaɓe. Don haka ku ɗauki wannan aiki da muhimmanci.”