Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya ce zaben da aka yi a ranar Asabar da ta gabata na Mista Abiodun Oyebanji na jam’iyyar APC a matsayin wanda zai gaje shi zai tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar.
Gwamna Fayemi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Ado-Ekiti mai dauke da sa hannun Mista Yinka Oyebode, babban sakataren yada labaransa.
- Masu Son Shiga Harkar Fim Su Riki Biyayya Da Kyau – Abba Harara
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Coci, Sun Kashe Mutane 3 A Kaduna
Gwamnan ya taya Oyebanji murnar fitowarsa a matsayin wanda ya lashe zaben.
Oyebanji ya lashe zaben ne da kuri’u 187,057, yayin da wanda ya zo na biyu, Mista Segun Oni na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), ya samu kuri’u 82,211, sai Otunba Olabisi Kolawole na PDP da ya samu kuri’u 67,457.
Fayemi ya bayyana nasarar Oyebanji a matsayin wanda ya cancanta.
“Wannan abin alfahari ne da ya dace ga mutumin da ya sadaukar da lokacinaa, kuzarinsa, basirarsa da dukiyarsa wajen ci gaban jihar nan cikin shekaru 30 da suka gabata.
“Mutanen Ekiti sun yi magana da babbar murya. Sakamakon zaben ya nuna cewa mutanen Ekiti mutane ne masu mutunci, a koyaushe suna goyon bayan shugabannin da suka yi musu hidima cikin aminci.
“Ba ni da tantama cewa zababben gwamnan zai yi wa mutanen Ekiti hidima kuma ya samar da damammaki ga sauran matasa.
“Babban yabo ya tabbata ga mutanen Jihar Ekiti na gari saboda nuna wayewa a lokacin yakin neman zabe,” inji shi.
Fayemi ya kuma jinjina wa INEC kan sabbin tsare-tsare da suka sanya aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci, da kuma yadda hukumomin tsaro suka tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.