• English
  • Business News
Friday, August 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyu Sun Tura Wa INEC Sunayen Masu Sa Ido 1,575,301 A Rumfunan Zabe 176,588

by Sulaiman
2 years ago
in Labarai
0
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa jam’iyyu 18 waɗanda su ka fito takarar zaɓen shugaban ƙasa, sun bada sunayen mutum 1,574,301 a matsayin wakilan sa-ido, wato ejan-ejan ɗin su a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.

Waɗannan adadin ejan-ejan su ne za su wakilci kowace jam’iyyya domin lura da yadda zaɓe ke gudana har zuwa lokacin tattara sakamakon zaɓe na kowane akwati da kowace rumfa.

  • INEC Na Sa Ran Karbar Sauran Kudaden Sallamar Ma’aikatanta Daga CBN Yau Talata – Okoye

Cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Litinin, ta ce daga cikin su akwai ejan-ejan masu lura da yadda ake tattara sakamakon zaɓe, wato ‘collation agents’ har 68,057 daga jam’iyyu daban-daban.

Labarai Masu Nasaba

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

Daga cikin ejan-ejan 1,574,301, NNPP ta tura wakilan ta na sa-ido har 176,200 a rumfunan zaɓe daban-daban a ƙasar nan.

Jam’iyyar LP ta tura ejan-ejan 134,874, PDP 176,588, APC 176,223.

INEC ta ce sauran jam”iyyu 14 kuwa sun tura adadin ejan-ejan na jimlar 910,426.

A ɓangaren ejan-ejan da za su lura da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe kuwa su 68,057, INEC ta ce NNPP ce ta fi sauran jam”iyyu yawan ejan-ejan a wuraren, domin ta na da 9,604.

Yayin da jam’iyyyar LP ke da ejan 4,859, ita kuwa PDP za ta tura guda 9,539, yayin da APC ke da 9,581.

Sanarwar INEC ta ce sauran jam’iyyu 14 na da jimlar ejan-ejan 34,474 kenan.

A Babbar Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Ƙasa a Ɗakin Taro na Duniya kuwa, jam’iyyun duka za su tura wakilai 27 jimla. PDP, APC, LP kowace wakilai biyu, NNPP wakili ɗaya, sauran jam’iyyu 14 kuma yawan na su wakilan guda 20 ne.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kotun Koli Ta Sanya Ranar 3 Ga Maris Don Yanke Hukunci Kan Tsarin Canjin Kudi

Next Post

Xi Jinping Ya Ba Da Umarni A Yi Namijin Kokarin Ceto Wadanda Suka Bace Sakamakon Rugujewar Mahakar Ma’adinin Kwal A Jihar Mongoliya Ta Gida

Related

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Manyan Labarai

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

3 hours ago
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 
Labarai

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

5 hours ago
Neja
Labarai

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

5 hours ago
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana
Labarai

Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

6 hours ago
NAF Ta Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Zamfara
Labarai

An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara

7 hours ago
Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin
Manyan Labarai

Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin

8 hours ago
Next Post
Xi Jinping Ya Ba Da Umarni A Yi Namijin Kokarin Ceto Wadanda Suka Bace Sakamakon Rugujewar Mahakar Ma’adinin Kwal A Jihar Mongoliya Ta Gida

Xi Jinping Ya Ba Da Umarni A Yi Namijin Kokarin Ceto Wadanda Suka Bace Sakamakon Rugujewar Mahakar Ma'adinin Kwal A Jihar Mongoliya Ta Gida

LABARAI MASU NASABA

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

August 7, 2025
Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

August 7, 2025
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 7, 2025
Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

August 7, 2025
Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

August 7, 2025
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

August 7, 2025
Neja

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

August 7, 2025
Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

August 7, 2025
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

August 7, 2025
Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

August 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.