Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce adadin masu sa ido na cikin gida da na kasashen waje sun kai 146,913, wanda za su sanya ido a babban zabe na ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga Maris.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja, a wajen wani taro na masu sa ido kan zaben da aka gudanar a cibiyar tattara bayanai ta kasa da kasa (ICC).
- Sin Ta Yi Kira Ga Al’ummar Kasa Da Kasa Da Ta Kara Mai Da Hankali Kan Batun Somaliya
- NNPP Ta Zargi DSS Da Firgita Mambobinta Da Kai Samame Ofisoshinta Na Kano
Farfesa Mahmood ya bayyana cewa, a bisa kyakykyawan tsarin a duniya, hukumomin zabe suna gayyaci kungiyoyi na cikin gida da na kasa da kasa masu sa ido kan harkokin zabe ko kuma shirya rangadin nazari ga manajojin zabe a lokacin zabe, yana mai bayanin cewa rahotanni da shawarwarin masu sa ido suna taimaka wa hukumar zabe wajen samun ci gaba mai dorewa.
Ya ce, “A zaben 2023, wanda za a fara a karshen makon nan na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, hukumar ta amince da kungiyoyin masu sa ido na cikin gida 196 wanda suka kasance guda 144,800.
“Hakazalika, hukumar ta amince da kungiyoyin kasa da kasa 33, inda ta suka turo masu sa ido 2,113. A dunkule dukkan kungiyoyi guda 229 ne masu sa ido, wanda suka kasance jimilla 146,913 da za su saka ido a zaben 2023.
“Wannan shi ne mafi girman yawan masu sa ido na cikin gida da na waje a tarihin zaben Nijeriya.”
Yayin da yake gargadin masu sa ido kan yin katsalandan a zaben, ya ce, “Ku masu saka ido ne kawai. Ka da ku tsoma baki cikin tsari ko nuna bangaranci. Bugu da kari, dole ne masu sa ido na kasa da kasa su kasance masu jagoranci ta hanyar cewa Tarayyar Nijeriya ce ke gudanar da zabukan wanda kuma ya zama dole a mutunta ‘yancin kai.”
Da take jawabi a wurin, Daraktar yankin Afirka na gidauniyar kasa da kasa kan tsarin zabe (IFES), Clara Cole, ta bukaci masu sa ido na kasa da kasa da na cikin gida da su bi dokokin INEC.
A halin da ake ciki, jam’iyyun siyasa 18 suka shiga zaben sun tura wakilan rumfunan zabe miliyan 1.5 da wakilai 68,057 domin gudanar da zabukan na ranar 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris.
Wannan yana kunshe ne a cikin rahoton da INEC ta fitar a daren ranar Litinin.
Rahoton ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da wakilai 176,588, sai jam’iyyar APC da 176,233, sannan jam’iyyar NNPP tana da 176,200, sai kuma jam’iyyar LP da ke da 134,874.