Kwamitin rabon asusun tarayya (FAAC), ya raba jimillar kudi na naira biliyan 750.174 ga matakai uku na gwamnati a matsayin rabon tarayya na watan Janairun 2023.
Daga cikin adadin kudaden da aka bayyana, wanda ya hada da na harajin kayayyaki, harajin tura kudi ta intanet, kirin kudi daga harajin da ba na ma’adinai, da karin naira biliyan 15.000 daga Ajiye, Gwamnatin Tarayya ta karbi naira biliyan 277.334, jihohin sun samu naira biliyan 244.975, kananan hukumomi sun samu naira biliyan 180.135, yayin da jihohin da ake hakar ma’adinan suka samu naira biliyan 32.730 a matsayin samar da ma’adinai na kashi 13 daga kudaden harajin ma’adinai.
- Yadda Gwamnonin Nijeriya Suka Butulce Wa Shugaba Buhari Bayan Ya Fitar Da Su Kunya
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
A cewar kamitin, kamar yadda ya bayyana a karshen mako, akwai karin naira biliyan 15,000 da za a raba shi daidai da matakan gwamnati uku.
Kwamitin rabon ya nuna cewa yawan kudaden shiga da ake samu daga harajin kayayyaki na watan Janairun 2023 ya kai naira biliyan 250.009, sabanin naira 250. .512 biliyan da aka raba a watan da ya gabata, wanda ya haifar da raguwar naira biliyan 0.503, daga wannan adadin an ware naira biliyan 10.000 daga harajin da aka karba, yayin da aka ba da naira biliyan 7.200 don zuwa jari da ajiye. Sauran kudaden da suka rage na naira biliyan 232.809 an raba su kamar haka; Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 34.921, jihohin sun samu naira biliyan 116.405, kananan hukumomi sun samu naira biliyan 81.483.
Don haka, Babban barajin da aka samu na naira biliyan 653.703 na watan wanda ya yi kasa da naira biliyan 1136.183 da aka samu a watan da ya gabata da naira biliyan 482.479. Daga wannan adadin na naira biliyan 23 da miliyan 494 aka bayar ga kudin tara da jimillar naira biliyan 241.091 don canja-canje, ajiye da maidowa. Sauran kudaden na naira biliyan 389.118 an raba su kamar haka; gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 189.745, jihohin kasar sun samu naira biliyan 95.227, kananan hukumomi sun samu naira biliyan 73.416, sai kuma karin kashi13 ga jihohin da ake hako ma’adinai wanda suka samu naira biliyan 32.730.
Har ila yau, an raba zunzurutun kudi har naira biliyan 13.799 daga cikin kudin harajin canjawa na intanet ga matakai uku na gwamnati kamar haka; gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 1.987, jihohi sun samu naira biliyan 6.624, kananan hukumomi sun samu naira biliyan 4.636, yayin da aka ware naira biliyan 0.552 harajin da aka karba.
Kwamitin ya kuma bayyana karin kudaden da aka ware na naira biliyan 100.000 daga kudaden shiga da ba na ma’adinai ba, wanda aka raba kamar haka; gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 52.680, jihohi sun samu naira biliyan 26.720, kananan hukumomi sun samu naira biliyan 20.600.
Harajin ribar man fetur (PPT), harajin kudi na kamfanoni mai da gas duk sun ragu sosai. Harajin kayayyakin ya ragu kadan-kadan. Yayin da harajin shigo da kayayyaki ya karu a wannan karo.
A cikin sanarwar, an fitar da jimillar kudaden shigar da za a raba na wannan wata na Janairu 2023 ne daga harajin da aka samu na kudaden shiga na naira biliyan 389.118, harajin kudi na BAT na naira biliyan 232.809, karin harajin da ba na ma’adinai ba na naira biliyan 100. 000, naira biliyan13.247 biliyan daga hada-hadar kudade na intanet da kuma karin naira biliyan 15.000 daga ajiya, wanda ya kawo jimlar rarraba kudade na watan zuwa naira biliyan 750.174.