Yau ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira wani taron manema labarai, inda ministan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Wang Zhigang ya bayyana halin da kasar ke ciki na inganta karfin kasar a bangaren kimiyya.
Wang Zhigang ya ce, matsayin alkaluman kirkire-kikire na kasar Sin ya tashi daga 34 a shekarar 2012 zuwa na 11 a bana, abin da ya almanta cewa, Sin ta shiga sahun kasashe dake karfi a fannin kirkire-kirkire a duniya. Matakin da ya bude wani sabon mataki na tabbatar da kai manyan matakan fasaha, da dogaro da kai wajen gina kasa mai karfin fasaha.
Ya kara da cewa, Sin ta nace ga ra’ayin hadin kan kasa da kasa a wannan fanni bisa ruhin bude kofa da yin hakuri da juna da cin moriya tare, inda ta kulla hulda da kasashe da yankuna fiye da 160 da shiga kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin bangarori daban-daban fiye da 200. Ta kuma ba da gudunmawa wajen hadin kan kasa da kasa kan tinkarar sauyin yanayi da samar da tsabataccen makamashi da kandagarkin COVID-19 da sauran muhimman bangarori. (Amina Xu)