Kasa da awanni a shiga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar, jam’iyyar APC a Jihar Abia ta dakatar dan takararta na majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa, Sanata Orji Ozor Kalu daga jam’iyyar.
Kalu wanda tsohon gwamnan Jihar ne Kuma yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar mazabar Abia ta Arewa a Majalisar dattabai kazalika yana rike da babbar mukami a Majalisar.
- UNWTO Ta Yaba Da Sake Bude Kasar Sin Don Yawon Bude Ido
- Abubuwan Da Suka Kamata A Sani A Kan Kada Kuri’a Ranar Zabe
Matakin jam’iyyar na kunshe ne a cikin wata wasika Mai dauke da sanya hannun gamayyar shugaban kwamitin ladabtarwa da da’a, Barr. Paul Nwabuisi; sakataren jam’iyyar na jiha, Chief Chidi Avaja, da shi kansa shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Kingsley Ononogbu.
A cewar wasikar, dakatarwar ta fara aiki ne nan take.
Kwafin wasikar wanda LEADERSHIP ta samu a ranar Juma’a a garin Umuahia, ta zargi Kalu, mai tsawatarwa na majalisar dattawan bisa zagon kasa.
“An dakatar da shi ne bisa shawarar kwamitin binciken da aka kafa a kansa daga gundumar Igbere A, a karamar hukumar Bende.”