A wannna makon mun tattauna ne da wani jarumi mai tasowa a bangaren wasan barkwanci na Kannywood, wato Yusuf Abubakar wanda aka fi sani da Jeje Arewa Commedian. Mataimakin Editanmu Bello Hamza, tattauna da shi ga kuma yadda hirar ta kasance:
Zamu so ka gabatar mana da kanka
Suna na Yusuf Abubakar,mutane kan kira ni Jeje Arewa Comedian
Wanne sana’a kake yi a halin yanzu?
A halin yanzu ina harkar wasan barkwanci ne, wato comedy, da fina finai a takaice dai ni jarumin fina finai ne, zan iya baka dariya a cikin ‘yan sekonni
To menene ya zaburar ko kuma ya karfafa ka har ka shiga wannan harkar?
Da farko dai na ji mutane na cewa, wasan barkwanci abu ne mai kyau, zai iya sa mutane nishadi a kowanne lokaci, na taba ji wani babban jarumi yana cewa, in har mutum ya ji dadin komedy, yana iya sauke wa masu hawan jini ga masu cutar hawan jini, wanann na daga cikin abin da ya kara karfafa ni, na kuma lura da cewa sana’a ce wanda zai iya daukaka ka, in Allah ya dafa maka, to tabbas za ka daukaka
Su wa kake koyi da su a cikin manyan masu wasan barkwanci a masana’antar Kannywood?
Cikin manyan jaruman da ke burgeni a Kannywood su hada da Ali Nuhu da Zango da TK dadin kowa.
Akwai wani kalubale ko tsangwama daga iyaye da abokanan zama da ka fuskanta tunda ka fara wannan harka na barkwanci?
Ba za a rasa kalubale ba amma a wurin iyaye na ban samu mastala ba, don na lura da cewa, a cikin harkar ban yi wani abin da ya saba wa addini ko al’adanmu ba to basu nuna min wani tsangwama ba ko su ce in daina ba.
Ko akwai wani alhairi da ka samu sakamakon wannan harka na wasan barkwanci wanda ba zaka taba mantawa da shi ba?
Lallai akwia alhairai masu yawa da na samu a wasan barkwanci da ba zan taba mantawa da suba, musamman alhairin da Albani ya yi mani, gaskiya mun ji dadi wannan al’amarin sosai, duk da bani kadai ya yi wa ba, a kungiyance ya bamu.
Wanne shawara kake da shi ga matasa musamman wadanda suke sha’awar shiga wannan harkar taku na wasan barkwanci?
Shawarana gare su shi ne su tabbatar da sun jajirce, su kuma sani cewa, sai ka zuba kudin ka sannan za ka kwashe, sai ka sa kudi da karfi da zuciya da rashin ganin kyashi, da rashin hassada, lallai duk wanda ya je neman shiga wannan sana’ar dole ya nisanci wadannan halayyar.
Akwai wani kira da kake da shi ga gwamnati, nata shigo domin tallafa muku a irin wannan harka da kuke yi na wasan barkwanci, musamman ganin cewa, harkar na sama wa matasa sana’a wanda ke rage zaman kashe wando a tsakanin matasan
Lallai ya kamata gwamnati ta shigo ta taimaka wa matasa masu irin wannan sana’ar, musammna ganin gwamnati za ta amfana da ayyukan matasan, don yawancin gwamnatin ne ke amfana da ayyukan matasa masu irin wannan aikin, inda suka janwo mu a jiki hakan zai kara mana karfin, muna mu ji cewa ana son mu ba wai a cigaba da tsananmu kawai ba.
Wane kira kake da shi ga matasa na su rungumi sana’o’in dogaro da kai komai kankantarsa saboda su tsira da mutuncinsu.
Tabbas zan yi kira ga matasa don ni na ga amfana da sana’a, sana’a na da matukar muhimanci, duk matsalar da ake fuskanta a gari mai sana’a baya rasa abin kashewa a hannunsa, yakamata matasa su rike sana’a komai kankantarsa, sana’a nada muhimmanci ya kuma da dadi.
Menene kololowar burinka a wannan sana’ar, me kake son ka cimma a sana’ar?
Bani da burin da wuce inga Allah ya azurta ni, ko ba ta wanna harkar ba don in taimaki talakawa da iyaye na, burina ke nan a rayuwa gaba daya.
Ina fatan in shahara a duniyar finafnai, kowa ya sanni gaba daya a duniya
Wanne jawabi kake da shi daga karshe?
Ina kira ga manyan a kannywood su rika januyo kananan jarumai masu tasowa a yi tafiyan da su don suma su amfana, a kuma rika gunadar da jarabawa kafin a sanya mutum a fim, hakan zai rage zargin cewa ana nuna son kai wajen sanya matasa a fim, da zargin ko wasu kudi suke bayar wa kafin a sanya su a fim, irin haka ke sa a wadanda basu kwarewa a fim daga baya a rika korafin cewa, fim ya lalace.
Ko akwi zargin cewa, sai an bayar da cin hanci kafin a sanya mutum a fim kenan?
A wasu lokutta a kwai irin wanna zargin, amma zairgi ne kawai da bashi da hajja, don ko muma ana zargin mu da cewa, muna karbar kudi kafin musa matasa a fim, don haka wannan maganar zargi ce kawai
Menene fatan ga Nijeriya?
Ina fatan Allah ya zaunar da kasar mu lafiya.