Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya gaza lashe akwatin mazabarsa, inda dan takarar shugaban jam’iyyar LP, Peter Obi ya lashe akwatin nasa.
Adamu, wanda ya kada kuri’arsa da misalin karfe 1:30 na rana, a rumfar zabe ta Angwan Rimi mai lamba 010 a karamar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa.
- Makamai Ba Za Su Tabbatar Da Zaman Lafiya Ba
- Zaben 2023: ‘Yan Daba Sun Sace Na’urar BVAS 8 A Delta Da Katsina
Jam’iyyar LP ta samu nasara da kuri’a 132 yayin da jam’iyyar APC ta samu kuri’a 85 a wannan rumfar.
A zaben Sanata ku2a, – APC (55), PDP (22), LP (42), NNPP (4), SDP (184), ADC (1), ZLP (3), yayin da aka samu kuri’u 7 marasa kyau.
A zaben dan majalisar dokoki da na tarayya kuwa: APC (46), PDP (41), LP (30), NNPP (4), AA (21), SDP (159), ADC (2), APGA (1), yayin da aka samu kuri’u 16 marasa kyau.
Da yake mayar da martani, Abdullahi Adamu ya nuna farin cikinsa kan yadda aka samu fitowar masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu.
Ya kuma nuna farin cikinsa kan yadda aka samu tsari mai kyau a bangaren tsaro.