Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ta dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya har zuwa ranar Lahadi a Yenagoa.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa INEC ta sanar da dage zaben ne a wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Asabar mai dauke da sa hannun, Wilfred Ifoga, shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar.
- Da Dumi-Dumi: Har Yanzu Jami’an INEC Ba Su Isa Rumfar Zaben Tinubu A Legas Ba
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dage Zaben Sanatan Enugu Ta Gabas
Wuraren da abin ya shafa sun hada da, Epie I da Epie III, Gbarain II da Okordia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarto daga shafin sadarwa na yanar gizo na INEC cewa, ba za a iya gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a fadin kasar a ranar Asabar din da ta gabata ba a yankuna hudu na Yenagoa, saboda masu zanga-zangar sun kawo cikas ga zaben.
NAN ya samu labarin cewa ana fama da karancin katin zabe a yankunan wanda ya sanya masu kada kuri’a gudanar da zanga-zanga a ofishin INEC na Yenagoa.
A lokacin da NAN ta ziyarci cibiyar rajista (RAC) da ke St. Peters a safiyar ranar Asabar, jami’an INEC sun gano cewa, katin zabe 1,500 ne kawai aka samu na masu kada kuri’a kusan 50,000 wanda hakan ya haifar da zanga-zanga.
Jami’an tsaron da ke cibiyar sun yi harbin gargadi don tarwatsa jama’a amma abin ya ci tura domin masu zanga-zangar sun dage cewa hakkinsu ne na kada kuri’a.
Korafe-korafen Kwamishinan Zabe na INEC na Bayelsa, Alex Hart, da Kwamishinan ‘yan sanda sun yi wani taro da jama’a da jawabai amma sun yi kunnen uwar shegu yayin da suka mamaye ofishin INEC.