Jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da za su yi aiki a rumfar zaben da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba su isa wajen rumfar zaben ba.
Rumfar zaben da ke matsugunin zabe mai lamba 047, a gundumar 3, Sunday Adigun, Alausa, a karamar hukumar Ikeja a jihar Legas.
- Yadda ‘Yan Nijeriya Ke Shirye-shiryen Shigowar Watan Azumi
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”
Zuwa karfe 8:41 na safiya, jami’an INEC ba su kuma kai kayan zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisar tarayya a wannan rumfar ba.
Talla
Cikakken bayani na tafe…
Talla