A kokarin da Mata ke yi na ganin ba abar su a baya ba wajan zaben wanda suke ganin shi ne zai fidda su daga cikin kunci rayuwa, Allah ya yi wa Shamsiya Ibrahim, rasuwa a runfar zabe mai Lamba 001 Asibitin kutate a mazabar Tsafe, cikin karamar hukumar Tsafe a loacin da ake shirin tantanceta domin kada kuria a mazabarta.
Shamsiya Ibrahim, ‘Yar mahaifar Tsafe ce kuma katin kuri’ar da na runfar Asibitin kutate ne a Tsafe, ta aure ce a Kwatarkwashi tazo dan kada kuri’arta a Mazabar mahaifarta ta Tsafe Allah ya amshi ranta.
- INEC Ta Dage Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisun Tarayya Zuwa Yau Lahadi Yenagoa
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dage Zaben Sanatan Enugu Ta Gabas
Adamu Yusif, ya bayyana wa wakilinmu cewa, Shamsiya Ibrahim, ta zo ne dama bata da lafiya, shigowarta ke da yuwa runfar zaben sai ta kama aman jini ta baki ta hanci.
An garzaya da ita zuwa Asibitin Dr Bawa wanda shi ne mafi kusa, inda anan Asibitin ya yi halinsa.
Mutuwar Shamsiya Ibrahim ta girgiza masu kata kuri’a a runfar zaben wanda ya yi sanadiyar sanya wasu fasa kada kuria sabo da jimamin rashinta.