Ofishin yada labarai na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, ya kira wani taron manema labarai a yau Litinin, inda ya bayyana cewa, a shekarar 2022, yawan kudin shiga da ko wanne mutum da ya fito daga kangin talauci a Xinjiang ya samu, ya kai RMB Yuan 14,951, wanda ya karu da Yuan 1608 bisa na shekarar 2021. Kuma alkaluman sun zarce yawan matsakaicin kudin shiga da daidaikun mutumin da ya fito daga kangin talauci a kasar ke samu da yuan 609, wanda ya karu da kashi 12.1 bisa na makamancin lokacin a 2021. Ban da wannan kuma, yawan karuwar ya zarce ta manoman kauyukan jihar da kashi 5.8%. (Amina Xu)