Dan takarar Sanata a jam’iyyar PDP na mazabar Enugu ta Yamma, Injiniya Osita Ngwu ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar.
Ngwu ya kayar da Sanata Ike Ekweremadu wanda shi ne Sanata mai ci tun shekarar 2003.
- Atiku Abubakar Ya Doke Tinubu, Obi Da Kwankwaso A Bauchi
- INEC Ta Ayyana Shekarau A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Sanatan Kano Ta Tsakiya
Ngwu, ya samu kuri’u 52,473, inda ya kayar da abokan takararsa da Dennis Amadi na jam’iyyar LP wanda ya samu kuri’u 48,053
Dan takarar APC Ezeh Chika kuwa ya samu kuri’u 3,825, inda kuma dan takarar NNPP Udeagulu Cletus ya samu kuri’u 1,052.
Jami’in zaben INEC na Enugu ta Yamma ne, ya sanar da sakamakon lashe zaben da Ngwu ya yi bayan ya aminta da sakamakon zaben.