Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana nasarar Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2023, a matsayin zababben shugaban kasa a tarayyar Nijeriya, a matsayin tabbatuwar dimokaradiyya ta gaskiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a ranar Laraba da ya fitar a Kano, ta hannun babban sakataren yada labaransa, Mista Abba Anwar.
- Lokaci Ya Yi Da Zan Sanya Kowa Farin Ciki A Nijeriya —Tinubu
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Ayyana Bola Tinubu A Matsayin Sabon Zababben Shugaban Kasa
Ganduje ya yaba da gwagwarmayar siyasa da jajircewar daular siyasar Tinubu, wadda ta samar da wasu abubuwan ci gaba ga al’ummar kasar nan, wajen tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa ya samu nasara baki daya.
“Sahihin hannun jarin Tinubu a cikin dan adam, ci gaban kasa da hadin gwiwar kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen fifita shi ga dukkan sassan kasar nan,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Yakin da Tinubu ya kwashe shekaru da dama yana yi na maido da mulkin dimokuradiyya a kasar nan, ‘yan Nijeriya sun fahimta sosai. Don haka, muna ganin hikima da kuma dalili mai kyau na jingina makomarmu gare shi.”
Yayin da yake tabbatar da cewa, zababben shugaban kasar zai bullo da dabarun tunkarar matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan, Gwamna Ganduje ya yaba wa shugabannin jam’iyyar da mambobin jam’iyyar da suka tsaya tsayin daka har zuwa wannan lokaci.