Wata kotun majisteri mai zamanta a Unguwar Normans land da ke Kano, ta tura Hon. Alhassan Ado Doguwa, gidan gyaran hali sakamakon zarginsa da harbe wasu mutane da kone su ranar Lahadin data gabata.
Ana zargin Alhassan Ado Dogwa, wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Nijeriya da laifin harbi tare da kone mutane a karamar hukumarsa ta Tudun Wada da ke jihar Kano.
- An Kama Alhassan Doguwa Kan Zargin Kisan Kai A Kano
- An Kona Motoci Da Jikkata Wasu Yayin Artabu Tsakanin Magoya Bayan NNPP Da APC A Tudun Wada
Alkalin kotun mai lamba 54 ya ce, za a ci gaba da shari’ar Doguwan ranar 7 ga wannan watan da muke ciki.
A yamma cin yau Laraba aka gurfanar da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Nijeriya, Hon. Alhassan Ado Doguwa, bisa laifuka da suka hada da haÉ—in baki wajen aikata kisan kai.
Sauran laifukan da ake zarginsa da su sun haÉ—a da raunata mutane da dama tare da zargin hannu a kunna wuta a ofishin jam’iyyar hamayya ta NNPP.
Ana zargin Doguwar da laifin tayar da gobarar a ofishin a ranar Lahadi 26 ga watan Fabarairu, 2023 wanda hakan ya yi sanadin ƙona wasu mutane da ke cikin ofishin.
Laifukan da ake zargin sa da su sun haɗa da kashe wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a ranar 26 ga wannan watan nan a lokacin da ake karɓa da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.
An yi ta yaÉ—a hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta, daga nan kuma rundunar ‘yan sandan ta gayyaci É—an majalisar domin gudanar da bincike kan batun.
Sanarwar ta ce bayan da É—an majalisar ya Æ™i amsa gayyatar ne, rundunar ‘yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.