Kotun shari’ar musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Murja Ibrahim Kunya, hukuncin sharar Asibitin Murtala na tsawon sati uku tare da zuwa Hisba tsawon watanni shida.
Aminu BBC da Ashiru Idris Mai Wushirya da Sadik Sharif za su yi sharar Masallacin Murtala har tsawon sati uku.
Tun da farko dai kotun ta tura Murja zuwa gidan yari na wucin gadi kafin yanke mata hukunci.
- Atiku Zai Yi Jawabi Da Yamma Kan Faduwa Zaben Shugaban Kasa
- Masana Sun Yi Martani Kan Tuhume-Tuhumen Da Ake Yi Wa Alhassan Ado Doguwa
Wasu Malaman Shari’ar Musulunci a Kano sun shigar da kara kan Murja, inda suka zarge ta da bata tarbiyya a kafar TikTok.
An dai kama Murja ne a otal din Tahir da ke Kano yayin da ta ke kokarin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta a jihar.
Daga bisani aka sake kamo wasu daga cikin matasan da ke amfani da kafar ta TikTok, sannan aka tisa keyarsu zuwa gidan yari.
Wannan dai na daga cikin shirin masu ruwa da tsaki da ke jihar don ganin sun tsabtace kafofin sada zumunta.