ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Sun Yi Martani Kan Tuhume-Tuhumen Da Ake Yi Wa Alhassan Ado Doguwa

by Sadiq
4 years ago
Masana

Rundunar ‘yansanda ta Jihar Kano ta gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan kasar Alhassan Ado Doguwa a gaban kotun majistire ta jihar, bisa tuhumar sa da hannu a tarzomar zabe, inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu a yankin mazabarsa.

Mallaka da amfani da makami babu izini, tsarawa da hada baki wajen aikata miyagun laifuka, kisan kai da kuma tada hankalin jama’a, suna daga cikin abubuwan da aka tuhumi Alhassan Ado Doguwa a zauren kotun.

  • Buhari Zai Kaddamar Da Aiki Sannan Ya Gana Da ‘Yan Kasuwar ‘Monday Market’ A Borno 
  • Peter Obi Da Jam’iyyarsa Ta Labour Sun Ce Su Ne Suka Yi Nasara A Zaben Shugaban Kasa Ba Tunibu Ba

Lauya mai gabatar da kara Barrister A’isha Salisu, tace rahotan farko na binciken ‘yan sanda ya nuna akwai zargi akan Alhassan Ado Doguwa, na cewa ya hada baki da wani mai suna Bashir Dahiru na kauyen Jammaje, da Bala mai Doki, da Hamisu Musa, da Nazifi Asananic, da Abdullahi Haruna, da kuma karin wasu da dama da yanzu haka ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo bayan da aka ce sun tada fitina ta hanyar cinna wuta a sakatariyar NNPP ta karamar hukumar Tudunwada ta yankin kudancin Kano.

ADVERTISEMENT

Kazalika, ana tuhumar Alhassan Ado Doguwa da raunata wani mai suna Alhassan Muhammad Sarkin Fawa da wasu mutane da dama, kana ya harbi wani Ibrahim Danbala, bayan haka ya jikkata wani Auwal Dauda ya kuma raunata wasu mutane da wuka.

Tun da fari dai Alhassan Ado Doguwa ya fada wa kotu cewa, yana muradin a karanto masa tuhume-tuhumen da harshen Hausa zalla maimakon yaren turanci, bukatar da kotun ta amince da ita nan take.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Daga bisani dai lauyan Alhassan Ado Doguwa Barr Abdul Adamu, ya roki kotun ta bashi belinsa, la’akari da matsayinsa a majalisar wakilan Najeriya, amma Barr Aisha Salisu ta soki yunkurin bada belin.

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, ya bada umurnin a tsare Alhassan Ado Doguwa a gidan Kurkuku. Yana mai cewa la’akari da girman laifukan da ake tuhumar dan majalisar tarayyar, kotunsa ba ta da hurumin yin shari’ar, amma ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga wannan wata na Maris, kuma ana sa ran gabanin lokacin an sami karin bayanai da shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar Kano.

Yanzu haka dai masana a fannoni dabamdaban na tsokaci akan wannan batu.

Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce matakin ya fara nuna cewa ‘yan sanda sun fara yin aikin su yadda ya kamata kuma hakan zai zama darasi ga ‘yan siyasar da ke sha’awar yin abin da ake zargin shi Alhassan Ado Doguwa da aikatawa.

Shi kuwa lauyan kare hakkin bil’adama Audu Bulama Bukarti, cewa yayi abin da ‘yansandan suka yi na gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu yana da kyau, amma sai bayan an tabbatar da hukuncin daya dace akansa bayan an tabbatar da laifi, san nan ne za a yaba wa ‘yansanda da alkalai.

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
Atiku Zai Yi Jawabi Da Yamma Kan Faduwa Zaben Shugaban Kasa

Atiku Zai Yi Jawabi Da Yamma Kan Faduwa Zaben Shugaban Kasa

LABARAI MASU NASABA

Masana

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Masana

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.