Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta ce ta ceto mutum 46 da dukiyar Naira miliyan 95.4 daga gobara 82 da aka samu a watan Fabrairu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ya fitar ranar Juma’a a Kano.
- Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 6 Kan Zargin Fashi Da Makami A Legas
Abdullahi ya bayyana cewa mutane 8 ne suka rasa rayukansu, yayin da gobara ta lalata dukiyoyin da ya kai Naira miliyan 31.8 a tsawon lokacin.
“Mun samu kiran agajin gaggawa 35 daga yankuna 13 a jihar,” in ji shi.
Kakakin ya shawarci mazauna Jihar da su rika kula da wuta domin kaucewa tashin wuta.