Wata babban kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a, Muhammad Nasir Yunusa, ta bayar da belin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa, Alhassan Garba Ado Doguwa kan kudi naira miliyan 500.
Kaalika, Kotun ta umarci Doguwa da ya gabatar da wasu masu tsaya masa mutum biyu da darajarsu ya kai wannan kudin.
- An Kama Alhassan Doguwa Kan Zargin Kisan Kai A Kano
- Jama’ar Tudun Wada Na Zanga-Zanga Kan A Yi Adalci A Zargin Kisa Da Ake Wa Doguwa
Doguwa na fuskantar shari’a ne kan zarge-zargen aikata manyan laifuka da suka kunshi hada baki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, kisan kai da kuma tada husuma a cikin al’uma.
Sai dai Alhassan bai amince kan cewa ya aikata laifukan ba lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotun majistire mai lamba 54 da ke Kano a makon jiya.
Lauyansa da ke ba shi kariya, Nuraini Jimoh (SAN), a ranar Litinin ya roki babban kotun tarayya da ke zamanta a Kano da ta amince da bayar da belin Doguwa, yana mai cewa ana kyautata zaton cewa wanda ake zargin bai da wani laifi lura da sashi na 35 na karamin sashi na 6 na kudin tsarin mulkin kasa (1999 da aka yi wa garanbawul).
Da ya ke yanke hukunci kan rokin, Alkalin Nasir Yunusa, ya amince da bayar da belin kan naira miliyan 500 da wasu mutum biyu masu daraja kamar ta kudin.
A cewar kotun, masu tsaya masa dole ne su kasance sarki mai daraja ta 1 ko manyan jami’an gwamnati.
Kotun ta kuma umarci Alhassan Doguwa da ya ajiye fasfo dinsa na fita kasar waje a wajen rijistaran kotun har zuwa kammala shari’ar.
Kotun ta kuma haramta wa Alhassan Doguwa zuwa mazabarsa a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi da ke tafe a ranar11 ga watan Maris na 2023.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, kotun majistire karkashin Ibrahim Mansur Yola, a ranar Larabar da ta gabata ya tura Alhassan Doguwa zuwa gidan yarin Goron Dutse bisa zarge-zargen da ake masa bayan kama shi da ‘yansanda suka yi.