Rundunar sojin Nijeriya a ranar Litinin ta tabbatar da shari’ar wani soja da ya harbe abokan aikinsa da kansa har lahira a sansanin Rabah, a Jihar Sokoto a ranar Lahadi.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana a Abuja cewa an fara bincike kan lamarin.
- Zaben Gwamna: NNPP Ta Gargadi Mambobinta Ka Da Su Yi Auren Siyasa Da Sauran Jam’iyyu
- Ana Goyon Bayan Bukatar Argentina Game Da Ikon Mallakar Tsibiran Falkland
Mwachukwu ya bayyana cewa, ba za a iya tantance halin da ake ciki a yanzu ba tunda sojan da ya kashe abokan aikinsa shi ma ya harbe kansa har lahira.
Ya kara da cewa babban hafsan soji na 8 da kuma kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji Manjo-Janar Godwin Mutkut da wasu manyan hafsoshi sun ziyarci wurin.
A cewarsa, GOC ya jajantawa sojojin da suka rasa abokan aikinsu a irin wannan yanayi mara dadi.
“Ya bukace su da su zama masu kula da ’yan uwansu kuma su ba da rahoton duk wani abin da ya faru da abokan aikinsu don hana sake faruwar wata barnar.
“Ya kuma kara musu kwarin gwiwa da su kwantar da hankalinsu da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
“Hukumomin Sojojin Nijeriya sun damu matuka game da wannan abu mai ban mamaki kuma sun kafa hukumar bincike (BOI) don bankado al’amuran da suka faru.
“Ana hasashen cewa sakamakon binciken BOI zai taimaka wajen dakile irin wannan mummunan lamari da ya faru a nan gaba,” in ji Nwachukwu.