Kwanaki kalilan da zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar Asabar mai zuwa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta umarci kwamishinan zabe (REC) da ke kula da Jihar Sokoto, Dakta Nura Ali, da ya tattara komatsansa ya fice tare da tsame hannunsa daga harkokin hukumar.
Haka nan kuma, tunin aka maye gurbinsa da sakataren gudanarwa ta hukumar a jihar, Hauwa Aliyu Kangiwa kuma hakan ya fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba.
- Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Harin Zamfara Da Kano
- Ka Daina Gararamba A Titi Ka Tafi Kotu —Martanin APC Ga Atiku
Wannan matakin na kunshe ne ta cikin wasikar daga Shalkwatar hukumar da aka aike jihar Sokoto da shi dauke da sanya hannun sakataren hukumar zabe ta kasa, Rose Oriaran-Anthony, mai dauke da kwanan wata 6 ga watan Maris 2023.
Sanarwar mai lambar alama: INEC/SCE/442/V.II, na cewa, “Ana sanar da kai (Dakta Nura Ali), kwamishinan zabe a jihar Sokoto (REC) cewa hukumar INEC ta cimma matsayar umartarka da ka gaggauta ficewa da yin nesa daga ofishin hukumar da ke jihar Sokoto cikin gaggawa har zuwa mataki na gaba”.
“An umarci Sakataren Gudanarwa da ta amshi ragamar kula da hukumar INEC a jihar Sokoto kuma hakan ya fara aiki ne nan take.”
A wasikun da wakilinmu ya ci karo da su da dama, sun nanata umarnin da aka bai wa sakataren gudanarwa Hauwa Aliyu Kangiwa da ta karbi cikakken ikon tafiyar da hukumar zabe a jihar Sokoto nan take har zuwa lokacin da hukumar INEC za ta fitar da wani sanarwar ko umarni daban.
Wasikar ta kuma umurce Hauwa da ta da ta tuntubi babban kwamishinansa ido na kasa, Farfesa Muhammad Sani Kaita, domin samun karin haske idan ta na bukatar hakan.
LEADERSHIP ta tuna cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne INEC ta sanar da cewa za a haramtawa duk wani ma’aikacin wucin gadi na hukumar muddin aka samu da sakaci da kauce wa ka’idar aiki a lokacin zaben shugaban kasa inda za a haramta masa shiga ko yin aiki a zaben Gwamnoni da ke tafe