Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh. Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da tsofaffin shugabannin Nijeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamsi Babbangida da janar Abdussalam Abubakar.
Wazirin na Adamawa ya gana da su ne a jiya laraba a garin Minna cikin jihar Neja.
Sai dai, ba a fitar da cikakkun bayanai dangane da ganawar ta su ta sirrin ba.
Bayan sun kammala ganawar ne Atiku ya wuce zuwa garin Yola jihar Adamawa.
Atiku dai na ci gaba da tuntubar manyan kasar nan dangane da zaben shugaban kasa da ya yi zargin an tafka magudi.