Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayar da damar yin amfani da katin zaben wucin gadi a zaben ranar 18 ga watan Maris na gwamnoni da ƴan majalisar dokokin jihohi.
Alkali Obiora Eguatu ne, ya bayar da umarnin a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da wasu fusatattun ‘yan Nijeriya da suka shigar ta neman a yi amfani da katin zaben wucin gadin a babban zaben a maimakon na din-din-din.
- An Yi Bikin Cika Shekaru 60 Da Sin Ta Fara Tura Tawagar Jami’an Lafiya Zuwa Ketare A Zimbabwe
- Mutum 14 Sun Jikkata Yayin Da Magoya PDP Da APC Suka Yi Arangama A Bauchi
Alkali Egwuatu, ya ce an bayar da umarnin ne kasancewar masu shigar da karar suna cikin kundin bayanan INEC.
Sai dai alkalin, ya ce bai amsa bukatarsu ta uku ba da ke neman a bai wa kowane dan kasa da ke da katin zaben wucin gadi damar kada kuri’a.
Da yake magana da ƴan jarida, lauyan masu karar, mista Victor Opatola ya ce hukuncin nasara ce ga duka ‘yan Nijeriya da suka sha wahalar yin rajista amma suka rasa samun katin zabensu na din-din-din kafin lokacin zaben.