Caji ofis din ‘yansanda da ke layin dogo a Jihar Lagos ya sanar da cewa, an cafke direban motar bas da ya dauko ma’aikatan gwamnatin jihar, biyo bayan taho mu gama da bas din ta yi da wani jirgin kasa da ke kan tafiyar sa a jiya Alhamis.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, fasinjoji shida ne suka mutu a hatsarin wanda aka dora laifin kan sakacin direban.
- Za Mu Tabbatar An Yi Zaben Gwamnoni Lafiya Ba Tare Da Tangarda Ba A Kebbi – ‘Yansanda
- Gwamnatin Kogi Za Ta Fara Hukunta Duk Wanda Ya Ki Karbar Tsoffin Kudi
Direban mai suna Oluwaseun Osinbajo, ya tuko motar ce daga yankin Isolo zuwa Alausa da ke Ikeja inda yaki tsayar da motar a kan hanyar ta layin dogo hakan ya janyo motar ta yi taho mu gama da jirgin kasan.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Yetunde Longe ne ya tabbatar da kama direban, inda ya ce, bayan sun gudanar da bincike da daukar sauran bayanai za su gurfanar da direban a gaban kotu.
Kwamishin ya ci gaba da cewa, amma kafin su gurfanar da shi a gaban kotun za su fara kai maganar a gaban daraktan gabatar da hukunci ganin cewa, direban ma’aikacin gwamnatin jihar ne.
Ya ce, rundunar na ci gaba yin bincike don gano yawan wadanda suka mutu a hatsarin, inda ya kara da cewa za kima a binciki gawarwarkin wadanda suka mutu.
Ya ce, yanzu zamu mika direban ga likitoci don su duba kwakwalwarsa ganin cewa, an tsayar da shi, amma yaki tsaya wa.