Wani yaro dan shekara 13 mai suna Ope Babalola a jihar Ogun, ana zargin sa da harbe wata yarinya ‘yar shekara 3 mai suna Esther Samuel.
An ruwaito cewa, lamarin ya auku ne a kauyen Kukudi da ke a karamar hukumar Yewa ta arearewa da ke a cikin jihar.
- Za Mu Tabbatar An Yi Zaben Gwamnoni Lafiya Ba Tare Da Tangarda Ba A Kebbi – ‘Yansanda
- Jami’in Afirka ta kudu: Tsarin Demokuradiyya Na Sin Ya Mayar Da Hankali Kan Jama’ar Kasar
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Abimbola Oyeyemi ya sheda wa manema labarai hakan a yau juma’a, inda ya ce, wanda ya mallaki bindigar mai suna Semiu Adegesin dan shekara 45 an kamo shi biyo bayan rahoton korafi da aka shigar a caji ofis din ‘yansanda na Imasayi kan cewa, wani yaro dan shekara 13 ya harbe wata yarinya ‘yar shekara 13.
Ya ce, biyo bayan karamin binciken, an gano cewa mai bindigar Semiu ya loda wa bindigar sa ta baushe albarusai, inda ya yi mata ajiyar sakainar kashi a bayan gidansa inda yara ke yin wasa, inda Ope ya dauki bindigar ya saita mariganyiyar da ta ya harba kunamar ta tashi ta kashe yarinyar.
Ya ce, an yi gaggawar kaita asibiti, inda a asibitin aka tabbatar da ta mutu, inda ya ce, ana ci gaba da gudanar da bincike.