Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, ta mayar da martani ga sanarwar da baitul malin kasar Amurka ya bayar ta shigar da wasu hukumomin kasar Sin cikin jerin sunayen ‘yan kasa na musamman da aka kebe domin kakaba musu takunkumi.
Kakakin ya bayyana jiya cewa, kasar Sin ta nuna adawa da yadda Amurka ta sanya kamfanoni 24 na kasar Sin da wani mutum guda, cikin jerin sunayen ‘yan kasa na musamman da aka kebe su domin sanya musu takunkumi, wadanda a cewar Amurka, suna shafar kasar Iran. Ya ce, ya kamata Amurka ta gyara kuskurenta, ta daina kara kuntatawa kamfanoni da ‘yan kasar Sin ba tare da wani dalili ba. Kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace don kare moriyar kamfanoni da daidaikun jama’ar kasar bisa dokoki.
Kakakin ya ce, takunkumin kashin kai da Amurka ta kakaba mata ya wuce kima, kuma ba shi da tushe a tsarin dokokin kasa da kasa, yana kuma matukar cutar da ‘yanci da muradun kamfanoni da daidaikun jama’ar kasar Sin. Haka kuma yana kawo cikas ga mu’amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sauran kasashe, da yin barazana ga tsarin samar da kayayyakin masana’antu ta duniya, tsaro da zaman lafiya da kawo cikas ga farfadowa da ci gaban tattalin arzikin duniya. (Zainab)