Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama wani tubabben mayaki na kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Alayi Madu, da kuma wani sarki mai sarautar gargajiya na Kajola, dake kan iyaka tsakanin Ondo da jihar Edo, Ba’ale Akinola Adebayo, kan ta’ammuli da haramtattun kwayoyi.
Suna cikin mutane 37 da aka kama da sama da tan 2.2 na haramtattun kwayoyi da jami’an NDLEA suka kama a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas da kuma samame a jihohi 12 a cikin makon da ya gabata.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce wannan nasara ce a wani bangare na ayyukan da ake yi na kawar da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.
Ya ce da sanyin safiyar Juma’a 10 ga watan Maris ne jami’an hukumar NDLEA suka kai wani samame a dajin Kajola da ke unguwar Kajola, inda suka lalata gonakin tabar wiwi guda uku masu girman hekta 39.801546.
An kama mai gonakin ne wanda ya yi ikirarin cewa shi ne Ba’ale na garin Kajola, Adebayo, mai shekaru 35 a gonar da misalin karfe 2:30 na dare, an kama shi tare da wasu mutane biyu da ake zargin ma’aikatansa ne: Arikuyeri Abdulrahman, dan shekara 23 da Habibu Ologun mai shekaru 25. an kama su ne a wata bukka da ke kusa da gonakin.
Hakazalika, wani matashi mai shekaru 26 Alayi Madu, wanda ya shafe shekaru 15 a kungiyar ta’addanci ta Boko Haram kafin ya mika wuya ga sojojin Nijeriya a shekarar 2021, jami’an NDLEA sun kama shi a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris a hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da haramtattun kwayoyi masu nauyin kilo 10, wanda ya ce ya saya ne a garin Ibadan na jihar Oyo zuwa Maiduguri, jihar Borno.