Sama da Limamai da Fastoci 30 suka halarci taron Bude baki na azumin da aka yi domin neman Allah ya kawo dauki kan matsalar tsaro da sauran abubuwan da suka addabi Jihar Kaduna wanda dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Mohammed Sani Sha’aban ya yi kiran a yi a jiya Litinin.
A bisa yunkurin da Hon. Sha’aban yake yi na ganin an samu nasarar kawo karshen duk wata ukuba da halin kuncin rayuwa a Jihar Kaduna, ya nemi a yi azumin inda dimbin al’umma suka amsa kira domin neman daukin Ubangiji dangane da yanayin halin rayuwa da al’ummar Jihar su ke ciki.
An gudanar da taron bude baki na shan ruwan Azumin ne a ofishin kamfen dan takarar dake garin Kaduna.
Da yake jawabi a wajen taron bude bakin Azumin, Dan takarar kuma Danburan Zazzau Sani Sha’aban, ya bayyana cewa wannan wani mataki ne da suka dauka domin neman kawo karshen halin ha’ula’i da al’ummar Jihar ke ciki sakamakon irin yadda al’amura na rashin kwanciyar hankali suke kasancewa.
Ya kara da cewa al’ummar Jihar ba su da wani karfi wanda ya wuci karfin Ubangiji kuma a dalilin hakan ne suka gudanar da wannan Azumin na musamman domin neman samun sauki a cikin rayuwar su da al’amuran Jihar Kaduna wanda hakan ke neman salwantar da rayuwar al’ummar.
“Ni mutumin Zariya ne kuma daga Zariya na Fito, kuma yanzu haka akalla sama da mutane Miliyan daya suka gudanar da wannan Azumin wanda mu ka yi bude baki a nan cikin cikin garin Kaduna.”
“Kuma a cikin garin Kaduna akalla sama da mutane Miliyan daya suka gudanar da wannan Azumin, haka a garin Zankuwa, Kafanchan da Kachia kuma muna saran Allah Zai dubi al’amuran mu ta hanyar da zamu samu saukin rayuwa.
Acewarsa, wasu da dama daga cikin al’ummar Jihar sun rasa ayyukan su, a yayin da wasu matasa suka kasa yin karatu sakamakon karin kudin wanda hakan yasa iyayensu basa iya biyan kudin makarantarsu.
Ya ci gaba da cewa akalla kusan kwanaki casa’in kenan da aka yi garkuwa da yan Uwansu wadanda suka hada da Sadiq Ango Abdullahi, MS Ustaz da sauran al’umma a harin Jirgin Kasa, to amma har yanzu Gwamnatin ta kasa yin komai domin ganin an sako su.
Honarabul Sha’aban, ya kara da cewa ya shigar da kara kotu domin neman hakkin shi a bisa karfa-karfan da aka yi masa a lokacin zaben fidda gwani na Jam’iyyar ta APC, kana ya aika da sakon neman ita Uwar Jam’iyyar ta dauki matakin da ya dace na ganin cewa ta daidaita al’amura a tsakanin duka Ya’yan Jam’iyyar.
Hakazalika, ya yi nuni da cewa masu zaben ‘yan takara mutane 1224 da suka sayi fom din zama masu zaben yan takara ba a basu dama ba, su ma sun shigar da kara kotu domin neman hakkin su bisa rashin adalcin da aka yi musu da tauye musu hakki a lokacin zaben.
A karshe, Sani Sha’aban, ya bayyana cewa suna sa ran wannan Azumin da suka gudanar kuma su kayi tawassali da ita, zai zame musu wata silla na samun waraka bisa duk wata damuwar da ta addabe su a ciki da wajen Jihar ta Kaduna.