• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Janye Wa Kowa Takara Ta Ba A Kaduna -Dan Takarar Gwamnan LP

by Sadiq
3 years ago
LP

Dan takarar gwamna na jam’iyyar LP a Jihar Kaduna, Mista Jonathan Asake, ya ce bai janye wa kowa takararsa ba a zaben gwamnan da za a yi ranar Asabar.

Asake, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kafanchan, hedikwatar Karamar Hukumar Jema’a ta jihar.

  • ‘Yansanda Sun Cafke Mataimakin Shugaban APC Na Jihar Edo
  • DSS Ce Abokiyar Hamayyar Mu A Jihar Kano Ba APC Ba – NNPP

A cewarsa, zargin cewa ya karbi Naira miliyan 100 daga hannun Uba Sani, dan takarar gwamnan APC, da Gwamna Nasir el-Rufai don hada kai wajen kayar da PDP a ranar Asabar a matsayin labari mara tushe.

“Suna sanya guba a zukatan mutane cewa Uba Sani ne ke daukar nauyina domin a raba kuri’un Kudancin Kaduna, don Uba Sani ya yi nasara.

“Babu wani daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP da zai iya fuskanta ta ya nemi na hakura da takarara, a maimakon haka sai suka koma yin amfani da ‘yan takara don ganin na sauka daga takara,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Ya kalubalanci jam’iyyar PDP ko kuma duk wanda ke da shaidar cewa ya karbi kudin da ya bayyana su a bainar jama’a.

Dan takarar jam’iyyar LP ya ce a matsayinsa na daya daga cikin manyan masu sukar gwamnatin APC a jihar, ba zai taba shiga wata yarjejeniya ta siyasa da Uba Sani ko El-Rufai ba.

“Suna so su gamsar da masu zabe cewa kuri’ar jam’iyyar LP kuri’a ce ta APC.

“Duk wadannan labarun karya ne. Ban taba zama ba kuma ba zan taba zama da Uba Sani da Nasir El-Rufai kan kowace irin yarjejeniya ta siyasa ba.

“Ina kalubalantar kowa da ya zo da wata kwakkwarar shaidar da muka taba haduwa inda na karbi kudi a wurinsu,” in ji shi.

Asake ya yi alkawarin samar da ingantaccen shugabanci kuma abin koyi ga al’ummar Jihar Kaduna idan aka zabe shi a ranar Asabar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
Manyan Labarai

Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Next Post
Gwamnatin Osun Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Hutu Saboda Zabe

Gwamnatin Osun Ta Ayyana Ranar Juma'a A Matsayin Hutu Saboda Zabe

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.