A shirye-shiryen zaben ‘yan majalisar dokokin jihar da za a yi a ranar 18 ga Maris, Gwamna Ademola Adeleke ya ayyana ranar Juma’a 17 ga Maris, 2023 a matsayin ranar hutu a Jihar Osun.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mallam Olawale Rasheed ya raba wa manema labarai a Osogbo, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa hutun na jama’a ne domin bai wa al’ummar jihar damar zuwa rumfunan zabe domin kada kuri’a a ranar Asabar.
- Ban Janye Wa Kowa Takara Ta Ba A Kaduna -Dan Takarar Gwamnan LP
- ‘Yansanda Sun Cafke Mataimakin Shugaban APC Na Jihar Edo
Gwamnan ya kuma shawarci mazauna jihar da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda yayin da suke shirye-shiryen gudanar da zabe.
“Ina kira ga al’ummar Osun da su fito fili su yi amfani da ‘yancinsu.
“Wannan zaben yana da matukar muhimmanci saboda za ku zabi ‘yan majalisa da za su yi aiki tare da ni.
“Dole ne ku zabi shugannin da suka dace,” in ji gwamnan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp