Kimanin na’urar 22 ta tantance masu kada kuri’a, BVAS, a Jihar Ribas na zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya ake fargabar bacewarsu.
Kwamishinan zabe na jihar, Johnson Alalibo, ne ya shaida wa manema labarai da wakilan masu sa ido kan zaben cewa sama da na’urori 6865 da aka tura jihar.
- Ana Korafin Rashin Fara Aikin Zabe Da Wuri A Bauchi
- ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kai Wa Ayarin El-Rufai Hari
An tattaro cewa uku daga cikin na’urar BVAS da aka amince da su sun lalace ba tare da gyara su ba, don haka ba za a iya amfani da su wajen zaben ba.
Alalibo ya ce ci gaban da aka samu ba zai shafi tsarin ba saboda hukumar zabe ta INEC tana da isassun tsare-tsare.
Ya kara da cewa wadanda suka bata ba za su dagula aikin ba.
Ya ce alkalan zaben za su tabbatar da cewa wadanda suka bace ba za su yi amfani ba.
Hukumar ta INEC ta kara da alkawarin cewa za a saka sakamakon zaben cikin lokaci guda bayan kammala zaben, tare da tabbatar da gudanar da sahihin zabe.
Sai dai wakilin YIAGA Afrika na jihar Obinna Ebogidi ya bukaci INEC da ta tabbatar da cewa alkawarin da suka yi na samar da isassun na’urori ya kamata ya tabbata.
Ebogidi ya ce: “Hukumar ta gaya mana cewa 22 daga cikin na’urorin BVAS sun bata yayin da “an sake fasalin na’urar BVAS 6865 gabanin zaben ranar Asabar.
“Damuwarmu ita ce a fara fitar da sakamakon zabe daga rumfunan zabe da wuri domin kaucewa sake faruwar abin da ya faru a zaben da ya gabata.”