Jami’an ‘yansanda a Jihar Imo sun ceto ma’aikatan hukumar INEC 19 da aka yi garkuwa da su da sanyin safiyar Asabar a jihar.
A cewar jami’an, ma’aikatan INEC 19 na wucin gadi ne aka sace a kan hanyarsu ta zuwa rumfunan zabe daban-daban guda bakwai da ke mazabar Ugbelie a karamar hukumar Ideato ta Kudu ta Jihar Imo.
- Da Dumi-Dumi: An Kama Shugaban Karamar Hukumar Da Kuri’an Bogi A Nasarawa
- Da Dumi-Dumi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti, Egbeyemi, Ya Rasu
Mai magana da yawun hukumar ta INEC, Chinenye Chijioke-Osuji, ya ce an ceto mutanen ne bayan kiran gaggawa da kuma bayanai kan lamarin da aka yi wa jami’an, inda nan take suka dauki matakin da ya dace.
Ta kara da cewa, duk da cewa an ceto su, ba a kwato dukkan kayayyakin zaben da suka hada da BVAS da wasu muhimman abubuwa ba.