Aliko Dangote ya yi murabus daga shugabancin kamfanin siminti, wanda ya kafa kuma ya gina ya zama mafi girma a nahiyar Afirka.
Ya ajiye muƙamin ne domin ya mayar da hankali kan aikin matatarsa ta man fetur, masana’antar sinadaran roba da taki, da kuma hulɗarsa da gwamnati.
- 2027: Masu Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP Sun Kara Matsa Kaimi Bayan Ficewar Atiku
- Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
An naɗa Emmanuel Ikazoboh, ɗaya daga cikin mambobin hukumar gudanarwar kamfanin, a matsayin sabon Shugaban kamfanin.
Hajiya Mariya Aliko Dangote ta shiga cikin hukumar gudanarwar kamfanin, bayan ritayar Farfesa Dorothy Ufot.
A lokacin shugabancin Dangote, kamfanin ya samu riba mai yawa, ya ƙara yawan fitar da kaya zuwa ƙasashen waje, tare da faɗaɗa ayyukansa a sassa daban-daban na Afirka.
Ikazoboh, ya ce ya jin daɗin samun wannan dama, kuma zai yi aiki tuƙuru don rage farashi da kuma amfani da makamashi mai tsafta.














