Rahotonni daga Jihar Kano sun nuna na cewa an ga wasu da ake zargin wakilan wasu jam’iyyun siyasa ne na raba atamfa da yaduka har ma da kudi a matsayin hasafin siyasa don su zabi dan takararsu.
An ruwaito an hangi yadda mutane suke karbar irin wadannan atamfofi, yayin da wasu kuma suka ki karba.
‘Yansanda Sun Ceto Ma’aikatan INEC 19 Da Aka Sace A Imo
Ina Da Kwarin Guiwar Lashe Zaben Gwamnan Bauchi -Sanata Jika
Jihar Kano dai na daya daga cikin jihohin da ake ganin zaben gwamna zai yi zafi sosai tsakanin ‘yan takara.
Ana ci gaba da fafatawa tsakanin jam’iyyun siyasa da ke jihar.
Amma masana harkar siyasa a Jihar Kano sun yi has ashen cewar zaben za a fafata ne tsakanin Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.