Jakadiyar kasar Birtaniya a Nijeriya, Catriona Laing, ta janye kalamnata na taya ‘yar takarar gwamnan jamiyyar APC ta jihar Adamawa Aishatu Dahiru Ahmed (Binani).
A jiya lahadi ne dai Catriona a kafar ta sada zumunta ta Twitter ta wallafa taya Binani murnar lashe zaben, inda ta ce, Binani ta zamo ‘yar takara mace ta farko da ta zamo zababbiyar gwamnan jihar Adamawa.
- Dan Takarar Gwamnan Labour Party Ya Janyewa Binani Takararsa A Jihar Adamawa
- Ganduje Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Sanar Da Nasarar Lashe Zaben Abba Gida-Gida
Sai dai, da safiyar yau litinin kwamishinan ta cire bayanin na ta da wallafa a kafar ta Twitter bayan ta gano cewa, ba a riga an kammala tattara sakamakon zaben ba.
Bisa ga alkaluman hukumar INEC, sun nuna cewa, gwamnan jihar mai ci kuma dan takarar PDP Umaru Ahmadu Fintiri na gaban Binani da kuri’u, inda sakamakon zaben karamar hukuma daya ne a safiyar yau litinin ya kasance ake dako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp