Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sanar da al’umar jihar cewa, jami’an tsaro a jihar na ankare domin dakile dukkan wata barazanar karya doka da oda a daukacin fadin jihar.
Kwamishin kula da harkokin cikin gida da harkar tsaro, Samuel Aruwan ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda sanarwar ta ce, biyo bayan samun rahotannin sirri da yinkurin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na tunzura jama’a don a tayar da hargisi a cikin jihar da kuma wasu sassan jihar.
- An Shiga Firgici Bayan Jin Karar Harbin Bindiga Kusa Da Ofishin INEC Da Ke Jihar Taraba
- Da Dumi-Dumi: Kakakin Majalisar Dokokin Zamfara Da Mataimakinsa Sun Sha Kaye
A cewar sanarwar, jami’an tsaro na kan gudanar da bincike kan wadannan rahotonin da mutanen da ke son tayar da hargisi a cikin jihar.
Sanarwar ta ce, jami’an tsaro na kan gudanar da bincike kan wannan rahotannin don hukunta masu hannu kan tayar da hargitsi.
Gwamnatin Jihar ta haramta nuna wata murna bayan an lashe zabe a jihar, inda gwamnatin ta roki ‘yan jihar da su sanar da bayanai masu barzana ga zaman lafiya a jihar ta hanyar kiran lambar waya kamar haka; 090340000.