An yabawa rukuni na 10 na likitocin kasar Sin, kan yadda ya gudanar da aikin jinya ga fiye da mutane dubu 2 da ke zaune a kusa da rijiyoyin mai na Paloch, da ke gundumar Melut na jihar Upper Nile na kasar Sudan ta Kudu.
Kwamishinan gundumar Melut, Deng Jok Angok, ya yaba wa tawagar likitocin kasar Sin din, kan yadda ta ba da shawarwari da magani kyauta ga fararen hula masu rauni, wadanda galibi suka dogara da asibitin sada zumunta na Paloch don kula da lafiya.
Ya ce, galibin fararen hular yankin matalauta ne, kuma suna fuskantar wahalar zuwa Juba, babban birnin kasar domin neman magani. Ya kara da cewa ziyarar da tawagar likitocin kasar Sin ta kai yankin daga ranar 15 zuwa 18 ga watan Maris ta sauya rayuwarsu.
Tawagar likitocin dai ta kunshi kwararru 13, wadanda suka hada da likitan gama gari, da likitan fida, da likitan mata, da likitan fata, likitan kunne, hanci da makwogwaro (ENT).
Tawagar ta ba da magunguna fiye da 200 ga majinyata dake yankin, da yin gwajin jini don gano cutar zazzabin cizon sauro, da magance radadin ciwo ta hanyar maganin gargajiya na kasar Sin (TCM), da caccaka allura, da ba da kulawar musamman ga wadanda ke fama da matsala ta tagayyara. (Ibrahim Yaya)