‘Ya’yan jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin jihar domin neman a ayyana dan takararsu Isah Ashiru a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
A ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King
- NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya
Sani ya samu kuri’u 730,002, babban abokin hamayyarsa – Ashiru na PDP – ya samu kuri’u 719,196.
Amma ba su gamsu da sakamakon ba, masu zanga-zangar wadanda galibinsu mata ne sanye da bakaken kaya, sun yi zanga-zangar zuwa sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya reshen Jihar Kaduna.
Sun zargi INEC da marawa Uba Sani baya.
Wadanda suka jagoranci zanga-zangar akwai tsohuwar Ministar Muhalli, Laurencia Mallam da tsohuwar shugabar mata ta PDP a jihar, Aishatu Madina.
Sun yi Allah-wadai da ayyana Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da INEC ta yi, tare da cewar ba shi ne muradin al’ummar Jihar Kaduna.
“Dalilin da ya sa muka taru a yau shi ne mu bayyanawa duniya rashin jin dadinmu kan sakamakon zaben Jihar Kaduna,” in ji ta.
“Kowa ya san abin da aka bayyana ba wakilcin abin da al’ummar Jihar Kaduna suka zaba ba ne. Abin da ya sa muka zo nan shi ne mu jawo hankalin hukumomin da abin ya shafa, wato INEC da ya kamata ta dauki wannan aiki da su yi abin da ya kamata da kuma nuna wannan amanar da ‘yan Nijeriya suka damka musu.”
Madina ta bayyana cewa, bayanan da aka dora a na’urar sakamakon sakamakon INEC (IReV) sun nuna cewa PDP ce ta lashe zaben gwamna a Kaduna.
Ta yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki a jihar da ta amince da cewa mutanen Kaduna sun zabi PDP.