Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya amince da fitar da kimanin naira biliyan daya domin biyan kudaden rajista da alawus-alawus ga wasu dalibai marasa galihu.
Babban Sakatare na Hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Sakkwato, Alhaji Bello Isa, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da jaridar Daily trust a Sakkwato, ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da daliban da gwamnati ke daukar nauyin karatun su aciki da wajen kasar nan.
Isah ya bayyana cewa an ware Naira miliyan 188.5 domin biyan kudin rajista ga dalibai 5,643 sabbi da tsoffi a Jami’ar Jihar Sakkwato (SSU) da kuma naira Miliyan N312.9m ga dalibai 7,096 na Jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUS) da ke Sakkwato.
Ya kara da cewa an amince da Kashe dala 89,100 da fam 15,000 a matsayin kudin alawus ga wasu dalibai a cibiyoyi daban-daban a Kasar Landan, Canada da sauran kasashen duniya.
Sakataren ya ci gaba da cewa, an amince da kashe dala 570,000 domin biyan kudin karatu da alawus ga sabbin dalibai da tsoffi da ke karatun likitanci bangare daban-daban a Jamhuriyar Sudan.
Ya ce Gwamna Tambuwal ya kuma amince da sake tura dalibai ‘yan Jiharsa da aka kwaso daga Ukraine sabida yaki, domin ci gaba da karatunsu a wasu kasashen.