Tsohon babban kwamandan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya yi kira ga tsaffin ‘yan ta’addar da har yanzu suke cikin dazukan jihar Borno da yankin tafkin Chadi da su ajiye makamansu su mika wuya domin samun zaman lafiya.
Rugurugu, a cikin wani sakon bidiyo mai tsawon sa’a 1 da dakika 54 da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda LEADERSHIP ta samu, ya tabbatar wa ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP cewa ba za a cutar da su ba idan suka mika wuya suka fito daga dazukan, inda ya ce shi kansa yana jin dadin zaman lafiya tun bayan amincewa da tayin afuwar da gwamnatin Nijeriya ta yi.
- Mayakan Boko Haram 443 Sun Mika Wuya Yayin Da ISWAP Ta Kashe Musu Sama Da Mutum 300
- ISWAP Ta Kashe ‘Yan Gudun Hijira 35 A Jihar Borno
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Adamu Rugurugu ya yana daga cikin tubabbun ‘yan ta’addar Boko Haram, wanda ya kai matsayin Kwamandan Yaki, mai ba da shawara ga shugabannin Boko Haram.
Adamu ya kwashe shekaru 10 yana yaki a kungiyar Boko Haram, yana daga cikin mutanen farko da suka amince da tayin afuwar da gwamnati ta yi don ci gaban da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
Rugurugu a cikin sakon bidiyo da ya aikewa ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP ya ce: “Ni ne mutumin da aka fi sani da Malam Adamu Rugurugu, ina so in yi kira ga ku (Boko Haram/ISWAP) da ke cikin dazukan da sakonnin ku dawo kamar yadda nake magana da ku, sama da shekara biyu da tubana yanzu, babu abin da ya same ni sai zaman lafiya kuma kowa ya shaida hakan.
“Ina so in faɗakar da ku waɗanda har yanzu suke cikin dazuka, na san yawancinku sun san ni. To me kuke yi har yanzu? Ya kamata ku fito.