Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da ‘Abba Gida-Gida’ na babbar jam’iyyar adawa ta NNPP ya karbi shaidar lashe zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Bayan kammala raba shaidar cin zaben ga wakilan majalisun kananan hukumomin Jihar Kano, sai babban Kwamishinan Hukumar zaben Jihar kano tare da jagoran da ya jagoranci tattara sakamakon zaben da kuma shugabannin sassan hukumomin tsaro suka gabatar da zababben Gwamnan Jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusif wanda aka fi sani da ‘Abba Gida-Gida’ inda aka damka masa takardar shaidar lashe zaben a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano.
- Ahmed Musa Ya Kamo Tarihin Da Zidane Ya Kafa A Kwallon Kafa
- An Yanke Wa Da Nijeriya Hukuncin Daurin Shekara 4 Saboda Damfara A Amurka
Da yake gabatar da jawabin godiya jim kadan da karbar takardar shidar tasa, injiniya Abba Kabir Yusif, ya bayyana farin cikinsa tare da mika saqon godiya ga al’ummar Jihar Kano bisa amincewar da suka nuna na zabarsa a matsayin Gwamnan Jihar Kano, haka kuma ya gode wa Hukumar Zabe, Jami’an tsaro ‘yan jaridu da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar har zuwa lokacin da aka tabbatar da samun wannan nasara.
Haka kuma ya mika godiyarsa tare da jinjinawa kokarin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bisa tsayuwar daka da ya yi har Allah ya tabbatar da wannan nasara.
Abba Kabir Yusif, ya jadadda alkawarin da ya yi na tabbatar da sake fasali tare da inganta harkar ilimi, lafiya, muhalli, tsaro da ingnata harkar masana’antu a Jihar Kano, saboda haka sai ya bukaci sauran abokan da suka yi takara da shi da cewa su taho domin hada hannu wajen ciyar da Jihar Kano gaba.
A karshe ya godewa iyayen kasa, Malamai da sauran masu yi wa Jihar Kano fatan alheri bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar tare da alkawarin cewa da yardar Allah jam’iyyar NNPP ba za ta ba su kunya ba.