Tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Timi Frank, ya danganta bayanan Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta yi kan kafa gwmnatin rikon kwarya a kasar nan a matsayin wani shiri na kitsa kama dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar LP, Peter Obi, kafin zuwan ranar 29 ga watan Mayu, 2003.
Timi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, a martanin da ya mayar wa hukumar.
- Li Qiang: Kwarin Gwiwar Da Kasar Sin Ke Da Shi Ya Kasance Jigo Wajen Kiyaye Zaman Lafiya Da Ci Gaba A Duniya
- NDLEA Ta Cafke Wata Matar Aure Tana Sayar Da Tabar Wiwi Lokacin Azumi A Katsina
A ranar Laraba ne, DSS ta zargi wasu kan yunkurin yi wa dimokaradiyyar kasar nan zagon kasa da kuma kitsa dakatar da mika mulki don kafa gwmnatin rikon kwarya.
Sai dai, Frank ya bayyana cewa, ikirarin na DSS ta yi shi ne kawai don kama masu son yin zanga-zanga kan magudin zabe da suke zargin an yi a zaben shugaban kasa na 2003, da kuma yunkurin cafke ‘yan adawa a kasar nan.
A cewarsa, bayanan sirri da DSS ta yi ikirarin ta samu na bogi ne kuma yunkuri ne kawai don kama masu son yin zanga-zanga kan zababben na shugaban kasa na 2003 da aka tabka magudi da kuma shirin kama ‘yan adawa kafin zuwan ranar 29 ga watan mayun 2003.
Ya bayyana cewa, kamata ya yi hukumar ta yi amfani da irin wannan bayanan na sirri da ta yi ikirarin samu don dakatar da yadda ‘yan ta’adda a kasar nan suka shafe shekaru suna kashe ‘yan Nijeriya.
Timi ya ce, a zahirance hukumar DSS ce ke son yiwa mulkin demokiradiyya zagon kasa a yanzu kan shirin da kitsa na son kama Atiku da Obi da kuma wasu manyan ‘yan adawa a kasar nan.
A cewarsa, ina kwarewar hukumar ta ke bayan shugaban hukumar zabe ta kasa farfesa Mahmoud Yakubu ya bayar da kai bori ya hau wajen yin magudin zabe a 2003.
Ya ce, muna son mu yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga kasashen duniya da su sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka wa DSS birki kan yunkurin yiwa demokiradiyya zagon kasa