Kafa karfaffar gwamnati wannan yana nufin gwamnatin da zata kunshi dukkannin abubuwan da suka kamata na wadanda za a zaba domin ayi ma al’umma ayyukan da suka dace ayi masu, yin hakan ba karamin aiki bane domin kuwa sai an bincika,da darjewa daga cikin gwarazan da ake dasu ganin tafiya da su zata iya haifar da da mai ido.Karfaffar gwamnati idan aka hada ta kowa zai ce gwamma ko gara da aka yi domin kuwa babu wanda zi iya kushe ta saboda wani nakasu da aka gano tattare da ita.Ayi ta maganar kai wannan gwamnati ai sam Barka Allah ya kara taimaka masu,ba wai ayi ta kuka ba da gwamnatin ba saboda wadanda ake ganin an kira domin su taimaka ayi tafiyar tare da su ba ma’aikata bane, su sun kasance wurin ne domin su azurta kansu ba su yi ayyukan da doka ta dora kansu ba.
Tun a shekarar 2022 data gabata ne majalisun kasa da suka hada dana Dattawa da Wakilai suka yi gyara akan wani sashe na tsarin mulkin kasa domin yin hakan zai basu dama ta sa idon akan ayyukan gwamnatoci da suka hada dana Tarayya da Jihohi suke yi,a wancan lokacin na majalisa ta 9, Shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan Shugaban majalisar wakilai ta Tarayya Femi Bajaamiala suka yi gyara a tsarin mulki, daga karshe majalisun biyu sun amince da gyaran nasu wanda kuma yin hakan ne ya nuna cewa Shugaban kasa ko gwamnoni dokar kasa bata basu damar kafa gwamnati ko fara yin aiki ba har abin ya zarce kwana sittin ba.Wannan yana nufin ke nan da zarar an rantsar da Shugaban kasa ranar 29 ga Mayu wato kamar sabon zababben Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da zarar an rantsar da shi ya fara aiki doka bata bashi damar zarce wa’adin kwana 60 ba,ba tare da ya nada Ministoci ba,wannan dokar haka take har ma gwamnoni suma bata ware su ba ta shafe su.
Sashe na 147 na tsarin mulki na kasa shi ya bada ita damar wato doka mai magana kan cewa da zarar an rantsa da Shugaban kasa ko gwamna to bai fa kamata ace ya wuce su kwanaki 60 ba tare da ya nada Ministoci ko Kwamishinoni wadanda za su taimaka ma shi wajen tafiyar da su ayyukan gwamnatin Tarayya ko na Jiha ba. Hakika kwanaki 60 sun isa ma Shugaban kasa yayi amfani dasu wajen neman sunayen wadanda yakamata suma suka kamata din a basu mukaman Ministoci da za su taya shi tafiyar da ayyukan cigaban kasa domin cancantar su.Zai yi hakan ne wajen zabo wasu ‘yan siyasa ne saboda ai sun taimakawa jam’iyyar ne musamman ma lokacin da ake ta fafutukar yakin neman zaben dantakarar jam’iyyar,wannan yana nufin irin gudunmawar da ya ba jam’iyyar ko ta shawara, kudade,ko kuma ya shiga duk wadansu abubuwan jam’iyyar da za ayi ayi su tare da shi.
Kamar yadda nace kwana sittin ko wata biyu ya isa a samu bayan an bincika sunayen wadanda za a ba mukaman na Ministoci,amma fa a lura kada a kai ga yin kamar yadda abinda ya faru lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashe kusan watanni shida yana neman wadanda zai ba mukaman Ministoci.Wani abu kuma sai bayan da Ministocin sun fara aiki bada dadewa sosai ba aka fara samun ‘yan guna- guni dangane da wasu daga cikin su.Domin gudun kauce ma irin hakan yanzu ya rage saura kamar wata biyu da ‘yan kwanaki, to idan aka hada da na wata biyu kamar yadda doka ta bada an samu wata hudu ke nan.Ya isa tun yanzu a fara nemada bincike na wadanda za a ba mukaman tun kafin ace wankin Hula ya kai dare don gudun kar a sake maimaita kamar yadda ta kasance a shekarun baya.
Duk wadanda za a ba mukaman Ministoci abu mafi dacewa shine kowanne daga cikin su a kai shi ma’aikatar ko fannin daya karanta zai fi yin amfani maimakon a kai shi wadda bai da wani abinda zai iya yi game da ma’aikata ko an tura shi can sai dai ayi ta harbarta Mati.Idan kowa aka kai shi ma’aikatar data dace da karatun da yayi abin zai fi armashi ba kamar yadda aka tura Dokta Christopher Ngige wanda shi kwararren Likita ne amma aka tura shi ma’aikatar kwadago maimakon a tura shi ma’aikatar lafiya wurin da ilmin su ko fannin da suka karanta yin hakan zai fi yin amfani.
Bugu da kari kuma duk wanda za a ba mukamin Minista matukar ya zo majalisar Dattawa domin tantancewa abu mafi kyau shine a tantance shi wajen yi mashi tambayoyi kan fannin daya karanta,ta haka ne za a iya gane ko kansa yana kawo wuta ko baya kawowa.
Bai dace ba ace ana nuna bambanci na tambayoyin da ake ma wadanda za a ba mukamin Minista domin wasu an ace masu ko mashi‘Take a bow and go” su nau’oin tambayoyin da aka yi ma wasu da su basu taba zama ‘yan majalisar ba,har ma ayi kamar ana son a kure shi wanda ya kasance a gaban ‘yan majalisar Dattawa lokacin da yake amsa tambayoyin da suke yi ma shi?ba domin komai ba sai don shi ko su basu taba zama ko dai dan majalisar Wakilai ko Dattawa a wani lokaci ba.Kamata yayi abinda ake yi ma Hussaini shi ma Hassan ayi ma shi irin hakan wannan shi ne adalci,saboda ai mutum bai tabbatar da dadin miya sai ya dandana ta tukuna.
A kan dauko wasu mutanen domin wata gudunmawar cigaban da suke yi ma al’umma da kudadensu,wasu kwararru ne ta fannoni na rayuwa daban- daban,sai wasu kuma Malaman jami’oi ne,kai da dai sauran mutane da suka bambanta sun kuma shahara ne wajen fannin da suka karanta,akan kuma jawo su ne domin ayi tafiya tare da su, yin hakan zai taimaka matuka ga cigaban kasa da al’ummarta.
Idan aka tashi zabar wadanda za a ba mukaman Ministoci ya dace abi cancanta ba kawai ayi amfani da domin shi ya ba jam’iyya gudunmawa ba ta kudi,bayan ga wanda ya dace a dauka daga Jiha amma an ki daukarsa domin shi ba dan jam’iyya mai rike da kambun mulki bane.
Kamata yayi abi cancanta kar kuma a nuna bambanci ga wani sashe a maida wasu sassan su zamanto ‘yan lele ko ace su ‘yan Mowa ne,wasu kuma a maida su ‘ya’yan Bora wadanda su dama ba son su ake yi ba,dole ne ake zama ko tafiya tare da su.
Duk mutumin da aka san baya da hali mai kyau nagari ko yana yin wadansu dabi’un da basu dace ace an ba shi mukamin Minista ba, kada aji kunyar cire sunan sa saboda barin ayi amfani da sunan sa wajen ba shi mukamin na iya samar da wata matsala.
Yakamata zabebban Shugaban kasa ya gane cewa dukkan ‘yan Nijeriya na shi ne wadanda suka zabe shi tare da wadanda basu zabe shi ba, shi na kowa ne ba tareda nuna wani bambanci na addini ko kabilanci ba,idan yayi haka wannan ya nuna ke nan shi da kan shi zai fara bude hanyar da zai fuskanci matsala daga farko har ya zuwa karshen mulkinsa.
Gwamnatin hadin kan ‘yan kasa ko sun zabe ka ko basu zabe ka ba kamar yadda na yi bayani sai an yi tafiya dasu,ai kai baka sani ba watarana suna iyayi maka abin kirki,ka taimaki wanda ka hadu da shi kan hanya lokacin da kake zuwa sama, baka sani ba lokacin da kake dawowa zuwa kasa watakila idan kun hadu a sama yana iya taimaka maka.
Koda ace an rantsar da Ministoci amma sai aka gane ya riga ya karya doka, kamata yayi kada ma a bata wani lokaci a cire shi daga mukamin domin ya nuna ba zai iya irin tafiyar da ake son ya yi ba.