Daga S.P Imam Ahmad Adam Kutubi
Idan mutum ya karya azuminsa da mantuwa, ko domin wani uzuri halattacce, zai rama azumi daya tak. Idan kuma ya karya shi ne da gangan, ko kuwa ya ki daukarsa ba da wani uzuri ba to, zai rama shi ta kowane hali, sannan kuma ya kara da yin kaffara. Watau ramuwa game da kaffara kenan. Kaffara ita ce mutum ya yi daya daga cikin wadannan abubuwa uku;
- Â Ko dai ya ciyar da miskinai sittin ko wanne ya ba shi mudu daya na abinci… kamar dawa ko gero ko dauro ko wake ko shinkafa ko alkama. Miskini shi ne mutumin da bai mallaki abincin kwana guda a jiye ba, kome lafiyar jikinsa. Wajibi ne a samu mutum sittin ba za a ba mutum talatin ba ko wanne mudu biyu, kuma ba za a ba da dafaffen abinci ba. Mudu shi ne abin da zai cika hannuwan mutum matsakaici bayan ya hada su wuri daya, bai matse su ba kuma bai bude su da yawa ba.
- Ko kuwa ya ‘yanta bawa, ko baiwa lokacin da yake akwai bayi, da sharadin bawan, ko baiwar, ya zama musulmi, lafiyayye, kuma cikakken bawa.
- Ko kuwa ya yi azumin wata biyu cif a jere ba yankewa. Idan ya sha daya da gangan, duk na baya sun baci, sai ya soma daga farko.
An ba mai yin kaffara zabi ya aikata duk wanda ya ga dama daga cikin ukun nan, sai dai ciyar da miskini ya fi lada, sa’an nan ‘yanta bawa ko baiwa, sannan yin azumin wata biyu..
Amai
Idan amai ya fito wa mutum bisa ga rinjaye ba da son ransa ba, har ya kawo ga bakinsa idan kam aman bai sake komawa ciki ba to azumi bai karye ba. Idan kuwa wani daga cikinsa ya sake komawa ciki ba a son ransa ba to azumi ya karye, zai rama guda daya. Idan kuwa da son ransa ne to zai yi ramuwa game da kaffara. Amma idan tun farko shi ne ya jawo yin aman nan da gangan zai rama azumi daya ko da wani abu bai koma cikinsa ba. Idan kuwa har wani abu ya sake komawa ciki da son ransa, ko da ba da son ransa ba zai yi ramuwa game da kaffara.
Jima’i
Idan mutum ya shigar da kan zakarinsa cikin farji da gangan, zai yi ramuwa game da kaffara, haka kuma ita ma macen. Amma da a ce mutum ya tarad da mace tana bacci, sai kawai ya auka mata da jima’i, duk babu azuminsu. Shi namijin zai yi ramuwa game da kaffara, macen kuma za ta rama azumi daya tak don rashin ganganci daga wajenta.
Fitar Da Maniyyi Ko Maziyyi
Idan mutum ya sumbaci mace, ko ya rungume ta ko ya yi wasa da ita ko ya yi mata mugun kallo na sha’awa, ko ya yi tunaninta a zuciyarsa, tunani mai zurfi, idan har maniyyi ya fito saboda yin daya daga cikin wadannan zai yi ramuwa game da kaffara. Idan kuwa maziyyi ne ne kawai ya fito zai rama azumi daya tak. Idan kuwa ba abin da ya fito to azumi bai baci ba, sai dai aikata dayan wadannan da rana haramun ne ga mai yawan sha’awa, makaruhi ne ga mai karancinta. Idan mutum ya yi baccin rana sai ya yi mafarki har maniyyi ya fito masa, babu komai, azuminsa bai baci ba.
Azumin Mara Lafiya
Wanda ya kamu da rashin lafiya idan ciwonsa yana da sauki zai dauki azumi, idan kuma ya ga yin azumi zai kara masa rashin lafiya ko zai sa ciwon ya yi jinkirin warkewa, to an halatta masa ya ci abinci, amma ya yi ramuwa. Kuma idan zai yiwu mutum ya ajiye maganinsa har da daddare ya sha, hakan nan zai yi. Idan kuwa ba hali. Zai sha abinsa da rana amma zai yi ramuwa.
Matafiyi
An halatta wa matafiyi, tafiya irin wadda ta halatta a gajarta sallah dominta, ya sha azumi amma ya rama. Yin azumi ga matafiyi shi ya fi idan zai iya. Idan mutum ya sha azumi ga tafiyar da ba ta cika sharudda ba, sai ya yi ramuwa game da kaffara.
Shigar Kwaro Baki
Idan wani dan kwaro kamar kuda ko makamancinsa ya yi sulu ya fada cikin bakin mutum, ya kuma wuce har ciki, azumi bai baci ba.
Tsufa Ko Ciwon Kishirya Ko Yunwa
Rududdugaggen tsoho ko tsohuwa da ba sa iya yin azumi domin tsufa, da mutum mai ciwon kishirwa ko yunwa, an yafe musu yin azumi. Sai dai kowannensu an so ya yi sadaka da mudu daya ko wanne maraice, har azumi ya kare. Idan kuwa mai ciwon kishirwa yana iya yin azumi a cikin wani yanayi na shekara, kamar lokacin dari ko marka, to, ya wajaba a gare shi ya rama azumin watan Ramadana a cikin lokacin. Wato lokacin sanyi ko lokacin ruwa. In dai za su iya wadannan lokuta to wajibi ne su rama abinda suka sha.
Sauran Bayani
Ya halatta ga mai azumi ya goge bakinsa da asuwaki wanda ba ya kakkaryewa cikin baki. Idan har ya kakkarye to sai ya furje guntayen a waje. Idan kuwa ya hadiye su da mantuwa ko bisa ga rinjaye, zai rama azumi daya. Idan kuma da gangan ne ya hadiyesu zai yi ramuwa game da kaffara.
Kurar hanya ba ta bata azumi ko da ta shiga ga makogwaro, idan garin abinci ko farar kasa, ko siminti, suka shiga makogwaron mutum azumi bai baci ba amma ga mutumin da yake aikinsa yana game da wadannan abubuwa kadai. Ga waninsa kuwa azumi ya baci.
Hayakin itacen wuta ba ya karya azumi amma hayakin taba ko na turaren wuta, ko tururin tukunyar dahuwar abinci, idan ya kai ga makogwaro azumi ya karye, sai a yi ramuwa.
Idan mutum ya face majina sannan ya sake hadiyeta da gangan azuminsa ya karye, sai ya yi ramuwa, idan ba da gangan ba ne kuma azumin sa yana nan. Amma idan mutum ya tattara yawu a cikin baki, sannan ya hadiye azumi bai karye ba amma yin hakan bai kamata ba.
Idan mutum ya ga alfijir yana fitowa alhali yana cin abinci ko yana shan wani abu, sai ya daina nan da nan. Idan ya daina azumi bai baci ba. Haka kuma idan jima’i ne yake yi sai ya cire zakarinsa da sauri, azumi bai baci ba. Idan bai cire ba zai rama azumi guda daya.