A ranar Asabar za’a ci gaba da buga wasannin mako na 29 a gasar Premier League ta kakar shekarar 2022 zuwa 2023 kuma Arsenal ce ta daya a kan teburi inda take da maki 69 da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City mai maki 61, mai rie da kofin a bara.
Za’a iya cewa kawo yanzu Arsenal wadda ke fatan lashe Premier League na bana a karon farko tana da sauran wasanni 10 a gabanta, kafin arare kakar bana kuma cikin wasannin da suka rage mata, za ta yi wasa biyar a Emirates, sannan ta buga sauran biyar a waje.
Cikin wasannin da Gunners za ta yi masu zafi har da wanda za ta kece raini da Manchester City da Liberpool da kuma Chelsea sannan Arsenal za ta buga wasan hamayya da West Ham a ungiyoyin birnin Landan da na alubale da Newcastle United.
Sai dai tuni ungiyar wallon afa ta Sporting Lisbon ta fitar da Arsenal a gasar Europa League, sannan Manchester City ta yi waje da ita a gasar cin kofin alubale na FA Cup.
Har ila yau, Brighton ce ta fitar da Arsenal a gasar League Cup na bana, yayin da Manchester United ce ta lashe Carabao Cup kuma hakan na nufin kofin Premier League ne kadai a gaban Arsenal da take son dauka, domin ta koma buga Champions League a badi.
Rabon da Arsenal ta lashe gasar Premier League tun kakar wasa ta 2003/04 arashin jagorancin tsohon kociyan ungiyar, Arsene Wenger, sai dai kuma duk da haka tana da kofin guda 13 jimilla.
Ungiyar wallon afa ta Manchester United ce kan gaba a yawan daukar firimiya ta Ingila inda take da guda 20, sai Liberpool mai 19 wadda ta lashe na 19 a shekarar 2020.
Wasa 10 da suke gaban Arsenal a Premier League:Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu. Arsenal da Leeds. Ranar Lahadi 9 ga watan Afirilu
Liverpool da Arsenal. Ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu. West Ham da Arsenal
Ranar Juma’a 21 ga watan Afirilu.
Arsenal da Southampton Ranar Laraba 26 ga watan Afirilu. Man City da Arsenal. Ranar Asabar 29 ga watan Afirilu.
Arsenal da Chelsea Ranar Lahadi 7 ga watan Mayu Newcastle da Arsenal. Ranar Asabar 13 ga watan Mayu.
Arsenal da Brighton. Ranar Asabar 20 ga watan Mayu. Nottingham Forest da Arsenal. Ranar Lahadi 28 ga watan Mayu Arsenal da Wolbes. Wasannin mako na 29 da za a buga a Premier League.
Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu Manchester City da Liverpool. Arsenal da Leeds United
Crystal Palace da Leicester City. Nottingham Forest da Wolberhampton Bournemouth da Fulham. Brighton da Brentford. Chelsea da Aston Billa. Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu. West Ham United da Southampton. Newcastle United da Manchester United
Ranar Lahadi 3 ga watan Afirilu Everton da Tottenham