Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, yayin taro na 52 na majalisar kare hakkin bil Adama ta MDD, kasar Sin ta gabatar da sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashe kusan 80, albarkacin cika shekaru 30 da zartar da sanarwar Vienna game da kare hakkokin bil Adama a duniya, tare kuma da gabatar da wasu shawarwari uku game da yadda za a aiwatar da sanarwar yadda ya kamata.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana yayin taron manema labarai na yau Juma’a cewa, shawarwarin sun hada da ya kamata a bayar da muhimmanci iri daya kuma bisa daidaito ga hakkokin raya tattalin arziki da al’adu da hakkokin jama’a da na siyasa da kuma hakkin samun ci gaba. Haka kuma, ya kamata a rika sanya jama’a gaba da komai, kana a yi watsi da rashin daidaito da inganta ci gaba mai inganci da ya kunshi kowa, kuma bisa adalci. Sannan kuma, a aiwatar da musaya da hadin gwiwa kan batutuwan kare hakkokin dan Adam bisa adalci da hadin kai da mutunta juna.
A cewar Mao Ning, a shirye Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen daukaka ka’idojin bai daya na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da adalci da demokradiyya da ‘yancin dukkan bil Adama, da kuma karfafa hadin kai da hadin gwiwa da watsi da ra’ayin fito-na-fito da na rarrabuwar kai, tare da hada hannu wajen aiwatar da shawarar ci gaban duniya da na tabbatar da tsaron duniya da ma shawarar wayewar kan bil Adama. (Fa’iza)