Masana kan harkokin Shari’a a Nijeriya sun bayyana cewa, bai kamata zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya fara tsoma baki kan harkokin gwamnati ba kafin mika masa mulki.
Masana shari’ar sun ce, duk da cewar Abba Kabir Yusuf na da damar bayar da shawara, amma ba shi da ikon bayar da duk wani umarni har sai ranar da aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar, kamar yadda Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana.
Zababben gwamnan, a baya ya shawarci masu gine-gine a filayen gwamnati da masu shirin bai wa gamnatin jihar bashi da su dakata, wannan kalaman da dukkan alamu ya fusata gwamnati mai mulki.
A nasa bangaren, gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi gwamnan mai jiran gado da cewa ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara.
Ganduje ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Hummad Garba ya fitar, inda yace, sabon gwamnan yana gaggawa.
Abba Hikima ya kuma ce daga yanzu har zuwa ranar rantsar da sabuwar gamnati, gwamna mai ci yana da ikon gudanar da duk abin da ya ga damar yi da ofishinsa.
Ya kuma ce duka yarjejeniyar da gwamnati mai ci ta zartar a yanzu halastacciya ce.
Sai dai kuma ya ce gwamnati mai jiran gado tana da damar da za ta warware duka yarjejeniyar.
To amma Barista Muhammad shu’aibu wani lauya mai zaman kansa a Abuja ya ce duk wata yarjejeniya matukar an yi ta bisa ka’ida to babu abin da zai iya tayar da ita.
Rahoton BBC Hausa.